in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sin da Rasha sun bayyana matsayinsu na rashin amincewa da kafa na'urorin kakabo makamai masu linzami a Koriya ta Kudu
2016-10-12 14:51:01 cri

A jiya Tatala 11 ga wata, aka ci gaba da gudanar da taron dandalin Xiangshan a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A yammacin wannan rana sojojin kasashen Sin da Rasha sun gudanar da wani taron manema labarai dangane da batun girke na'urorin kandagarkin makamai masu linzami. A yayin taron, batun wadannan na'urori sanfurin THAAD a kasar Koriya ta Kudu wanda ke jawo ce-ce-ku-ce ya kuma zama batun da bangarori daban daban ke tattaunawa a kai. Abokiyar aikinmu Lubabatu ta hada mana rahoto a kai.

A jiya da yamma ne, sojojin Sin da Rasha suka gudanar da wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ya ba wa jama'a mamaki.

A yayin taron, wakilin kasar Sin, manjo janar Cai Jun ya bayyana cewa, batun girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami ka iya yin babban tasiri ga huldar da ke tsakanin kasashen duniya ta fuskar zaman lafiya da tsaro da kuma aikin kwance damarar soja. A saboda haka, yadda kasar Amurka ke kokarin girke wadannan nau'rori, a bangare guda kuma zai gurgunta yanayin tsaro a duniya, kana zai iya tada wata sabuwar gasar kera makamai.

A game da yadda kasar Amurka ke shirin kafa na'urorin kakkabo makamai masu linzami a kasar Koriya ta kudu, ya jaddada cewa, "Kasashen Amurka da Koriya ta kudu sun tsai da kudurin girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin Thaad a Koriya ta Kudun, kuma wannan mataki zai lalata moriyar kasashen da suka hada da Sin da Rasha, don haka, kasar Sin ba ta yarda da wannan mataki ba, kuma tana kalubalantar Amurka da ta canja manufarta. Matsayin kasashen Sin da Rasha ya zo daya ko kusan daya a kan batun kafa na'urorin kakkabo makamai masu linzami, wato dukkansu sun ki yarda da kokarin wata kasa na girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami ba tare da iyaka ba."

A nasa bangaren, wakilin kasar Rasha, laftana Janar Victor Poznihir ya ce, Amurka tana kokarin kafa na'urorin kakkabo makamai masu linzami a sassan Turai da Asiya da tekun Pasifik ne a yunkurin dakile karfin sojan kasashen Rasha da Sin, ta yadda za ta inganta fin karfinta a duniya. Laftana Janar ya ce, "Mu da abokananmu na kasar Sin mun yi nazari a kan manufofin sojin Amurka ta fannin makamai masu linzami. Abin da nake son jaddadawa shi ne, tsarin kandagarkin makamai masu linzami da Amurka ke shirin kafawa ba alheri ba ne ga Rasha da kuma kasar Sin. Wai bisa dalilinta na barazanar da take fuskanta daga makamai masu linzami na Iran da Koriya ta Arewa, ya sa kasar Amurka ta kafa manyan makamai a wurin da ke dab da iyakar kasashen Rasha da Sin, amma wadannan makamai ba wai sabo da kandagarki ne kawai ba."

A watan Mayun bana, sojojin Sin da Rasha sun gudanar da atisayen soja a cibiyar nazarin kimiyya ta rundunar tsaron sararin sama ta ma'aikatar tsaron Rasha, a yayin taron, sojojin kasashen biyu sun sanar da cewa, a shekara mai zuwa, za su gudanar da atisayen soja game da dabarun kakkabo makamai masu linzami karo na biyu. Wakilin kasar Sin, manjo janar Cai Jun ya kara da cewa, "Sojojin kasashen Sin da Rasha sun bayyana amincewa da juna a atisayen da suka gudanar a wannan shekara game da kandagarkin makamai masu linzami, baya ga kasancewa wani sabon fanni na hadin gwiwa a tsakaninsu. Makasudin wannan atisayen soja shi ne horar da sojojin a fannin tsaron sararin sama da kandagarkin makamai masu linzami. Abin da za a jaddada shi ne, an gudanar da wannan atisayen soja ne ba sabo da wani bangare na uku ba. Yanzu haka kuma muna tuntubar bangaren Rasha a game da atisayen soja da za a gudanar a shekara mai zuwa."

A watan Yuli na wannan shekara, Amurka da Koriya ta Kudu sun sanar da kafa tsarin kandagarkin makamai masu linzami na THAAD a kasar Koriya ta Kudu, ba tare da la'akari da rashin amincewar da kasashen da abin ya shafa suka nuna ba, ciki har da kasar Sin. Manazarta suna ganin cewa, ba wai sabo da kare Koriya ta Kudu daga Koriya ta Arewa ba ne kawai kasar Amurka take shirin kafa wannan tsarin, a hakika, kafa tsarin THAAD zai iya inganta tsare-tsare na kakabo makamai a Asiya da tekun Pasifik, matakin da kuma zai iya taimaka mata wajen gudanar da leken asiri a kasashen Sin da Koriya ta Arewa da gabas mai nisa na Rasha gaba daya. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China