in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang yana rangadin aiki a Macao
2016-10-11 13:14:12 cri

Da tsakar ranar jiya ne, zaunannen mamban hukumar siyasar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma firayin ministan majalisar gudanarwar kasar Li Keqiang ya sauka Macao, yankin musamman na kasar cikin jirgin saman musamman domin fara rangadin aiki, tare kuma da halartar bikin kaddamar da taron ministocin dandalin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake magana da harshen Portuguese karo na biyar. Wannan ita ce ziyarar farko da Li Keqiang ke yi a yankin na Macao.

A yammacin wannan rana, firayin minista Li ya je hedkwatar gwamnatin yankin Macao bisa rakiyar gwamnan yankin Chui Sai On, inda ya bayyana cewa, yana fatan gwamnatin yankin zai ci gaba da aiwatar da manufofin "kasa daya, tsarin mulki iri biyu", kana "mazauna Macao su tafiyar da harkokin yankin da kansu", kana za ta ci gaba da aiwatar da manufa mai cin gashin kanta domin cimma burin samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki a yankin.

Li Keqiang ya bayyana cewa, tun ba yau ba ya ke son kawo ziyara yankin Macao, yanzu ya gani da idonsa irin babban sakamakon da gwamnatin yankin ta samu karkashin jagorancin gwamna Chui Sai On, yana mai cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin Macao a karkashin jagorancin gwamna Chui Sai On, ta yi nasarar dakile matsaloli da dama da take fuskanta bisa goyon bayan mazaunan yankin, lamarin da ya kai ta ga samun babban sakamako, musamman ma a fannonin raya tattalin arziki da kwanciyar hankali da kuma zaman jituwa a yankin, ana iya cewa, hakika gwamnatin Macao ta yi kokari,kuma gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta jinjina wa wadannan nasarori sosai."

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, ko da yake yankin Macao yana fuskantar kalubale yayin da yake kokarin samun ci gaba, amma a sa'i daya kuma, yana da damammakin samun bunkasuwa, Li Keqiang yana fatan yankin zai yi mafani da damammakin domin kara samun wadatuwa, alal misali, kara kyautata zaman rayuwar mazaunan yankin ta fuskar samar da gidajen kwana da abubuwan sufurin jama'a da sauransu, ta yadda za a sa 'yan uwa a Macao da yawansu ya kai dubu 650 su kara samun moriya daga manufofin kasar Sin. Li Keqiang ya ce, "Aiwatar da manufar kasa daya,mai bin tsarin mulki irin biyu zai kara kyautata aikin gwamnatin Macao, musamman ma wajen samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki da tabbatar da manyan tsare-tsaren kasar Sin da kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin Macao da sauran jihohin kasar Sin, ban da haka kuma, ana fatan yankin Macao zai kara bude kofofinsa wajen ba da ilmi ga yara da matasa da kuma horas da su yadda ya kamata."

Li Keqaing ya kara da cewa, kwanakin baya, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta tsara wasu manufofin ba da gatanci ga yankin Macao bisa la'akari da sabbin bukatun da yankin ya ke da su a halin yanzu, Li Keqiang ya ce, "Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin tana goyon bayan yankin musamman na Macao da ya shirya dandalin tattalin arzikin yawon bude idon kasashen duniya sau daya a kowace shekara, tana kuma goyon bayan yankin da ya shirya bukukuwan baje koli wadanda za su jawo hankulan kasashen duniya, tana kuma goyon bayansa da ya kafa wata cibiyar kudi ta musamman domin yin cinikin kasa da kasa da kudin kasar Sin RMB a Macao da kuma kafa asusun raya hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Portugal a Macao."

Kafin Li Keqiang ya ziyarci hedkwatar gwamnatin yankin,sai da ya hau hasumiyar yawon bude ido ta Macao domin kallon birnin daga sama, kana ya saurari rahotonnin da aka gabatar masa game da tsare-tsaren ci gaban yankin a cikin shekaru biyar masu zuwa, inda ya jinjinawa shirin da gwamnatin Macao ta tsara wajen ingiza bunkasuwar tattalin arziki da taimakawa bunkasuwar matsakaita da kuma kananan kamfanoni a yankin, kaza lika yana sa ran yankin Macao zai kara samun ci gaba wajen raya tattalin arziki da kwaciyar hankali da zaman jituwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China