in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF da Bankin Duniya sun yi kira da a yi yaki da ra'ayin kariyar ciniki
2016-10-10 13:34:22 cri

A jiya ne aka rufe taron shekara-shekara na asusun ba da lamuni na duniya IMF da na bankin duniya a birnin Washington na kasar Amurka. Sakamakon tabarbarewar yanayin tattalin arzikin duniya, mahalarta taron sun fi mai da hankali ne kan yadda za a samu ci gaba, da dakile ra'ayin nuna kariyar ciniki.

A yayin taron da ya gudana, shugabar asusun ba da lamuni na duniya Madam Christine Lagarde ta nuna damuwa kan yanayin da tattalin arzikin duniya yake ciki, ta ce,

"Mun ga yadda aka dade ana fama da tafiyar hawainiya ta fuskar ci gaban tattalin arziki, kana mutane kalilan ne suke amfana da tattalin arzikin. Wannan labari ba shi da dadin ji ko kadan, ganin yadda koma bayan tattalin arziki ya kan haddasa ta da zaune-tsaye a bangaren siyasa, lamarin da zai kara gurgunta tattalin arzikin duniya."

A yayin taron na bana, Madam Lagarde ta sha jaddada yanayin koma bayan tattalin arzikin duniya, da rashin daidaito tsakanin sassa daban daban, wadanda suka kasance manyan matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu.

A nata bangare, majalisar kula da harkokin kudade da harkar kudin duniya karkarshin laimar IMF ta ba da rahoton cewa, yanzu haka a duk duniya ana fama da matsalar kayayyakin bukatu, da lalacewar yanayin cinikayya, zuba jari, da masana'antu. Haka kuma siyasar wasu sassan duniya ta shiga halin ha'ula'i, lamarin da ya kara sanya fannin hada-hadar kudi shiga cikin hadari, gami da haddasa manufofin kariyar ciniki. Bisa la'akari da yanayin da ake ciki ne, bangarori masu halartar taron suka nanata bukatar dakile ra'ayin nuna kariyar ciniki, da kara bude kofar kasuwanni. Dangane da batun, Madam Lagarde ta kara da cewa,

"Mun san cewa, dunkulewar tattalin arzikin duniya ta amfanawa mutane da yawa. Don haka, ba ma ganin cewa ya kamata mu yi watsi da tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya. Maimakon haka, ya kamata mu ci gaba da wannan yunkuri, tare da bullo da wata manufa ta daban, wato kokarin kula da dukkan mutane, musamman ma wadanda tsarin da muke bi yanzu zai iya bar su a baya."

A nasa bangare, mista Jim Yong, shugaban bankin duniya, ya yi amfani da labarin yadda kasar Sin ta fitar da mutanen da yawansu ya kai miliyan 700 daga kangin talauci a matsayin wani misali, don nuna muhimmancin manufar bude kofa, da kokarin habaka cinikayya. Ya ce,

"Abin da za mu iya koya daga nasarar da kasar Sin ta samu shi ne, yadda kasar ta samu babban ci gaba a fannin rage talauci, yana da alaka sosai, da manufofin da kasar ta aiwatar na bude kofar kasuwanninta, da kokarin inganta harkar ciniki, wadanda suka ba ta damar takara da sauran bangarorin duniya."

A halin yanzu, kusan dukkan tattalin arzikin kasashe masu sukuni na tafiyar hawainiya, yayin da wasu kasashe masu tasowa kuma suke kan gaba wajen samun ci gaban tattalin arziki, lamarin da ya sa wadannan kasashe, musamman ma kasar Sin ke janyo hankali sosai a wajen taron, inda aka nazarci fasahohinsu na samun ci gaban tattalin arziki, da matakan da suka dauka don sauya tsare-tsaren tattalin arzikinsu.

Daga ranar 1 ga watan da muke ciki ne, a hukumance kudin kasar Sin RMB ya fara aiki a matsayin kudaden ajiya na ketare(SDR)na asusun ba da lamuni na duniya IMF, lamarin da ya taimaka wajen tabbatar da ingancin tsari na SDR, da tsaron hada-hadar kudin duniya. Dangane da batun, mista Zhou Xiaochuan, shugaban babban bankin kasar Sin, ya ce kasar Sin na son hadin gwiwa da sauran kasashe don daidaita yanayin tattalin arzikin duniya. A cewarsa, karuwar tattalin arzikin Sin tana wani matsayi mai dacewa, yayin da ake ganin alamar kyautatuwar yanayin tattalin arziki a kasar. Ban da haka, gwamnatin kasar Sin tana kokarin inganta tsare-tsaren tattalin arzikin kasarta, wanda zai samar da damammakin ci gaban tattalin arziki a kai a kai, sabo da haka tattalin arzikin kasar na da makoma mai haske cikin wani dogon lokaci mai zuwa.

Asusun ba da lamuni na duniya shi ma ya gaskata kamalan shugaban babban bankin kasar Sin, wanda ya ce nasarar da kasar Sin za ta samu ta fuskar sauya tsarin tattalin arzikinta za ta samar da karin gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China