A ranar Laraba ne, majalisu biyu na Amurka suka shure kujerar nakin shugaba Barack Obama bisa yawancin kuri'un da aka jefa. Shi dai Obama ba ya goyon bayan iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata su kai karar gwamnatin Saudiya. Sai dai wasu iyalan wadanda suka mutu sakamakon hadarin na ranar 11 ga watan satumba suna ganin cewa, kungiyar Al-Qaeda tana samun kudadenta ne daga kasar Saudiya, a saboda haka, ya sa dole ne gwamnatin Saudiya ta dauki alhakin abin da ya faru.(Fatima)