in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi liyafar cika shekaru 67 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a Najeriya
2016-09-30 08:54:20 cri


Ranar Alhamis 26 ga wata ne, ofishin jakadancin Sin dake Najeriya ya kira wata liyafa, domin murnar cika shekaru 67 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Manyan jami'an gwamnatin Najeriya da da dama sun halarci wannan liyafa. Ga rahoton da wakilinmu Murtala Zhang ya aiko mana.

Sabon jakadan kasar Sin dake Najeriya Mista Zhou Pingjian ya jagoranci liyafar, inda ya bayyana manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 67 da suka gabata, da kuma ci gaban dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Najeriya, da kuma Sin da Afirka baki daya.

Daga cikin manyan jami'an gwamnatin Najeriya da suka halarci liyafar, akwai karamar ministan harkokin wajen Najeriya Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, da ministan aikin gona Mista Audu Innocent Ogbeh, da shugaban hukumar kula da harkokin shige da fice Malam Muhammed Babandede, da shahararren dan siyasar kasar nan wato Sanata Shehu Sani da sauransu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China