in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudin RMB na kasar Sin zai shiga SDR
2016-09-29 11:15:05 cri

Ranar 1 ga watan Oktoba dake tafe, asusun ba da lamuni na duniya IMF zai sanya kudin RMB na kasar Sin cikin kudaden da za a rika amfani da su a fannin kudaden ajiya na ketare wato SDR a hukumance, adadin kudin na RMB zai kai kashi 10.92 cikin dari. Wannan mataki yana da muhimmanci matuka na shigar RMB cikin kasuwannin duniya, hakan ya nuna cewa, hukumomin kasa da kasa da sauran kasashen duniya sun amince da sakamakon da gwamnatin kasar Sin ta samu wajen yin kwaskwarima ga kudin nata, kuma hakan zai taimakawa ci gaban kasashe masu tasowa.

Tsarin SDR, wani tsari ne da asusun ba da lamuni na duniya IMF zai rika amfani da shi a fannin kudaden ajiya na ketare, yanzu tsarin yana kunshe da kudade hudu wato dalar Amurka da kudin Euro da Fam na Britaniya da kuma Yan na Japan. A ranar 30 ga watan Nuwamban bara wato shekarar 2015, shugabannin hukumar zartarwar asusun IMF suka amince da sanya kudin kasar Sin na RMB cikin wannan tsari, kuma sun tsai da kuduri cewa, tun daga ranar 1 ga watan Oktoban bana, za su shigar da RMB a cikin kudaden ajiya na ketare na asusun, kuma adadinsa zai kai kashi 10.92 cikin dari, wato adadin da zai kai matsayi na uku a cikin wannan tsari na SDR, a bayan dalar Amurka wanda ya kai kashi 41.73 cikin dari da kudin Euro mai kashi 30.93 cikin dari.

Shugabar cibiyar dake yin nazari kan zuba jarin kudin musanya ta kasar Sin Tan Yaling ta bayyana cewa, kudin RMB na kasar Sin ya samu karbuwa a kasashen duniya, hakan zai amfanawa ci gaban kasashe masu tasowa. Madam Tan ta ce, "Hukumomin kasa da kasa da kasashen duniya sun amince da kwaskwarimar da aka yiwa RMB, kuma sun amince da darajar kudin na RMB, kana bayan shigar RMB cikin kudaden ajiya na ketare, kudin na RMB zai kai matsayi na uku a bayan dalar Amurka da kudin Euro, lamarin da ya nuna cewa, kasashe masu tasowa suna samun bunkasuwa cikin sauri, kana zai kara taimakawa ci gabansu a nan gaba yadda ya kamata."

Gobe Jumma'a 30 ga wata, asusun IMF zai sanar da adadin kudaden dake cikin tsarin SDR, wanda zai nuna muhimamncinsu, Madam Tan Yaling ta bayyana cewa, darajar kudin RMB ta taka muhimmiyar rawa yayin da gwamnatin kasar Sin take kokarin shigar da RMB cikin tsarin na SDR. Tana mai cewa, "Gwamnatin kasar Sin tana kokarin kiyaye darajar musaya RMB, wato a cikin 'yan watannin da suka gabata, an kiyaye darajar musaya RMB wato dalar Amurka guda 1 tana daidai da kudin RMB 6.68, hakan ya taimaka wa kokarin da kasar Sin ke yi wajen shigar RMB cikin tsarin SDR."

Tun a watan Nuwamban bara ne, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai a jere domin tabbatar da burin shigar da RMB cikin tsarin kudaden ajiya na ketare, kuma asusun IMF ya yaba da kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi a wannan fannin.

Ana ganin cewa, shigar da RMB cikin tsarin kudaden ajiya na ketare wato SDR, zai kara habaka imanin kasuwannin duniya kan RMB. A halin da ake ciki yanzu, adadin kudin musayar da aka ajiye a fadin duniya ya kai kusan dalar Amurka biliyan dubu 10 da dari 9, an yi hasashe cewa, ya zuwa shekarar 2020, adadin kudin kasar Sin RMB da za a ajiye zai kai kashi 7.8 cikin dari. Shugabar ofishin kula da biyan kudade da kuma karbar kudin musanya ta hukumar kula da kudin musayar kasar Sin Wang Chunying tana ganin cewa, bayan da aka shigar da RMB cikin wannan tsari, masu zuba jari a ketare za su kara sayen kadarorinsu ba tare da wata fargaba ba. Madam Wang Chunying ta ce, "Masu zuba jarin kasashen waje za su canja wasu kadarorinsu zuwa kadarori na RMB, kuma za su kara sauyen wasu kadarorin RMB, misali asusun IMF da bankin duniya da sauran hukumomin kudi na kasa da kasa."

Bayan da RMB ya shiga tsarin kudaden ajiya na ketare, kasar Sin za ta samarwa asusun IMF kudi da RMB domin gudanar da ayyukanta, hakan zai sa adadin RMB da za a yi amfani da su a cikin asusun ya karu. Yanzu RMB ya riga ya kasance kudin da ake amfani da shi kamar yadda sauran manyan kudade. Shugabar cibiyar dake yin nazari kan zuba jarin kudin musanya ta kasar Sin Tan Yaling ta bayyana cewa, kamata ya yi RMB ya yi amfani da wannan dama domin kara taka rawa a cikin kasuwannin duniya. Tana mai cewa, "Ya kamata mu yi amfani da wannan dama wato shigar da RMB cikin tsarin kudaden ajiya na ketare domin kara habaka kayayyakin da kamfanonin kasar Sin suke samarwa a kasuwannin duniya, saboda hakan zai taimake mu wajen magance hadarin kudin da za a fuskanta, kana yana kyau mu kara la'akari da hakikanin yanayin da muke ciki, tare kuma da yin kwaskwarima, ta haka za a kara daga matsayi da darajar RMB a kasuwannin duniya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China