in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana da karfin yin takara a duniya
2016-09-28 11:05:18 cri

A yau Laraba ne, dandalin tattaunawa kan harkokin tattalin arzikin duniya (WEF) dake birnin Geneva na kasar Switzerland ya gabatar da rahoton karfin yin takara a duniya daga shekarar 2016 zuwa 2017, inda Sin ke matsayi na 28 a cikin shekaru uku a jere da suka wuce, kana tana sahun gaba a cikin kasashen BRICS. Kasar Switzerland ce ta ke matsayi na farko a cikin jerin shekaru 8.

Rahoton karfin yin takara a duniya yana daya daga cikin rahotanni mafi muhimmanci da dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya (WEF) ya ke gabatarwa a kowace shekara. An fitar da wannan rahoto ne bisa ma'aunin yin takara a duniya da aka gabatar a shekarar 2004, wanda ya kunshi fannoni 12. A bana, rahoton ya yi bincike kan kasashe da yankuna 138 a duniya, tare da gabatar da matsayinsu, a cikinsu kasashe da yankuna guda 10 dake kan sahun gaba su ne Switzerland, da Singapore, da Amurka, da Holand, da Jamus, da Sweden, da Birtaniya, da Japan, da yankin Hongkong na Sin, da kuma Finland.

Dandalin tattaunawar WEF ya bayyana cewa, a cikin wadannan kasashe da yankuna 10 dake kan sahun gaba, ko da yake yawancinsu kasashen Turai ne, amma akwai babban gibi a tsakanin kasashen da ke yankin kudanci da arewacin nahiyar Turai. Kasashen Spaniya da Italiya suna kasa da matsayi na 30, yayin da Greece ta yi kasa zuwa matsayi na 86. Kasar Faransa, ita ce kasa ta biyu mafi girma a cikin kasashen dake amfani da kudin Euro, kuma matsayinta ya daga zuwa matsayi na 21.

Bayan haka, rahoton ya ce, kasar Sin tana matsayi na 28 a cikin jerin shekaru 3, hakan ya sanya ta kasancewa a sahun gaba a cikin kasashen BRICS. Bisa ma'aunin karfin yin takara, Sin ta fi samun maka a fannonin girman kasuwanni, da yanayin tattalin arziki daga manyan fannoni, da kiwon lafiya, da kuma tarbiya a matakin farko. A sa'i daya, rahoton ya gabatar da manyan matsalolin da Sin ke fuskanta, wadanda suka hada da yanayin zuba jari, da rashin manufofi na dogon lokaci, da hauhawar farashin kayayyaki da dai sauransu. A cikin sauran kasashen BRICS kuma, matsayin Indiya ya taso zuwa na 39, yayin da Rasha ke matsayi na 43, sai kasar Afirka ta Kudu da ke matsayi na 47. Matsayin Brazil ya sauka zuwa 81, wadda ta zama kasa daya tak da ta matsayinta ya yi kasa sosai a cikin kasashen BRICS.

A bangaren kasashen Larabawa kuwa, an fi dora muhimmanci kan kyautata karfin yin takara sakamakon faduwar farashin makamashi. Rahotanni na bayyana cewa, duk kasashen dake fitar da makamashi a wannan yanki, dole ne su ci gaba da kokarin raya tattalin arzikinsu a duk fannoni. Ban da haka, kasar Rwanda ce ta fi samun ci gaba a cikin kasashen Afirka dake yankin kudancin Sahara, inda ta ke matsayi na 52.

Dadin dadawa, a cikin wannan rahoto, an gano cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, kasashen duniya sun fara rage bude kofofinsu ga sauran kasashen duniya, hakan ya kawo illa ga karuwar tattalin arziki da samar da sabbin kayayyaki a duniya. Mutumin da ya kafa dandalin tattaunawar WEF, kana shugaban gudanarwar dandalin, mista Klaus Schwab ya bayyana cewa, rashin bude kofa ga sauran kasashen duniya na kawo illa ga karfin yin takara, kuma wannan zai sa shugabannin kasashen duniya su gamu da matsaloli a kokarin da ake yi na samun dauwamammen ci gaba a duniya.

Bayan haka, rahoton ya yi karin bayani cewa, bai ga dalilin da zai sa kasashe masu sukuni za su kasa farfado da manufar daidaita tsarin harkokin kudi da sauransu da karuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci, sabo da bisa la'akari da kasashe da yankunan dake kan sahun gaba a cikin bayanin rahoton karfin yin takara a duniya, kasashe dake baya-baya sun dauki matakan da suka dace, amma ba tare da samun nasara ba. Wannan yana nuni da cewa, tushen karfin yin takara, shi ne ginshikin samun sakamakon mai kyau bayan daukar matakan harkokin kudi.

Rahoton ya kuma yi nazari kan yadda kasashe masu tasowa za su tafiyar da harkokinsu na tattalin arziki. Ko da yake muhimman kayayyakin amfanin jama'a, da kiwon lafiya, da tarbiya, da kasuwanni cikin yanayi mai kyau suna da muhimmanci sosai wajen samun makin karfin yin takara. Amma bayanai na nuna cewa, fasahohi, da masana'antu, da samar da sabbin kayayyaki da sauransu su ma suna da muhimmanci sosai wajen la'akari da ma'aunin karfin yin takara.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China