in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun raya Sin da Afirka yana taimakawa ga hadin gwiwar samar da kayayyaki tsakanin sassan biyu
2016-09-26 10:44:59 cri

Asusun raya kasar Sin da kasashen Afirka shi ne asusu na farko da kasar Sin ta kafa musamman domin zuba jari kai tsaye a kasashen Afirka, a cikin shekaru 9 da suka gabata wato tun bayan da aka kafa shi a shekarar 2007, asusun yana taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kamfanonin kasar Sin shiga kasuwannin kasashen Afirka. A ranar 22 ga wata wato ranar Alhamis da ta gabata, aka bude reshen asusun a birnin Nairobin kasar Kenya wanda ya kasance na biyar a jerin rassansa. Kwanan baya ne, wakilinmu ya yi zantawa da shugaban asusun Chi Jianxin domin jin ta bakinsa.

An kafa asusun raya kasar Sin da kasashen Afirka ne a shekarar 2007, yanzu an bude reshensa na biyar a kasar Kenya, kafin wannan kuma, an bude rassa guda hudu a kasashen Afirka ta Kudu da Habasha da Zambiya da kuma Ghana, reshen asusun, shi ne na biyu ne da aka bude a yankin gabashin nahiyar ta Afirka.

Yayin da yake bayani game da makasudin bude reshen asusun a kasar ta Kenya, shugaban asusun Chi Jianxin ya bayyana cewa, a cikin kasashe shida mambobin kungiyar tarayyar kasashen gabashin Afirka wato Kenya da Tanzaniya da Uganda da Ruwanda da Budundi da kuma Sudan ta Kudu, Kenya ce fi saurin samun ci gaban tattalin arziki, kana a cikin 'yan shekarun da suka gabata, huldar dake tsakanin Sin da Kenya ta yalwatu yadda ya kamata, alal misali, a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma ciniki, musamman ma tun bayan da aka gina layin dogo dake tsakanin biranen Mombasa da Nairobi, ana iya cewa, layin dogon zai taimaka matuka ga ci gaban tattalin arziki a Kenya, har ma a dukkanin kasashen dake yankin gabashin Afirka.

Chi Jianxin yana ganin cewa, Kenya tana mai da hankali sosai kan hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Sin wajen samar da kayayyaki, kuma ta riga ta samu sakamako a bayyane, a halin da ake ciki yanzu, adadin kamfanonin kasar Sin da suka zuba jari domin bude reshensu a kasar ta Kenya yana karuwa a kai a kai. Tambaya ita ce, ta yaya za a iya cimma burin samun moriyar juna tsakanin sassan biyu yayin da suke kokarin yin hadin gwiwar samar da kayayyaki, wato ba ma kawai hadin gwiwar za ta dace da hakikanin yanayin Kenya ba, har ma zai samar da damammaki ga al'ummun wuraren kasar su samu moriya daga fasahohin kasar Sin da kayayyakin kasar Sin? Kan wannan, Chi Jianxin yana mai cewa, reshen asusun da aka bude a Kenya zai ba da muhimmanci kan aikin asusun a cikin kasashe shida mambobin kungiyar tarayyar kasashen gabashin Afirka, reshen asusun da aka bude a Habasha kuma zai kula da aikin asusun a sauran kasashen dake gabashin Afirka, kana rassan nan biyu kuma za su yi hadin gwiwa a tsakaninsu domin samar da dammmaki ga kamfanonin kasar Sin kan yadda za su kara zuba jari a yankin gabashin Afirka.

Ya zuwa karshen watan Agustan bana, gaba daya adadin jarin da asusun raya Sin da Afirka ya zuba kan ayyukan 87 a kasashen Afirka 36 ya zarta dalar Amurka biliyan 3.5, sassan biyu wato Sin da Afirka suna gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin samar da kayayyaki da gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da makamashi da hako ma'adinai da aikin gona da sauransu yadda ya kamata, har ma al'ummun kasashen Afirka sama da miliyan 1 sun amfana daga gare su.

Chi Jianxin ya ci gaba da cewa, ko da yake ana tafiyar da aikin asusun lami lafiya, amma duk da haka yana fuskantar kalubale, misali, yayin da wasu kamfanonin kasar Sin suke zuba jari a kasashen Afirka, a wasu lokukan ma ba sa fahimtar manufofin kasashen sosai, a saboda haka, ana bukatar karin lokaci domin a kyautata aikin asusun.

Chi Jianxin ya ce, wani lokaci, bayan da aka kammala aikin, sai a gano cewa, muhimman kayayyakin bukatun jama'a kamar su samar da lantarki ko mai, da sharadin hanyoyi da sauransu ba su iya biyan bukatun amfanin aikin ba, wannan ya sa dole a jira, hakan ya sa wasu kamfanonin kasar Sin ba su yin wata-wata kafin su tsai da kudurin zabu jari a kasashen.

Kazalika, Chi Jianxin ya jaddada cewa, har kullum asusun raya Sin da Afirka yana nacewa ga manufarsa ta samun moriyar da za ta dace ta hanyar samar da taimako ga al'ummun kasashen Afirka, kafin 'yan kasuwa su zuba jari, sai sun mai da hankali kan moriyar al'ummun kasashen Afirka, wato suna ganin cewa, abu mafi muhimmanci shi ne bukatun wuraren da za su zuba jari.

Chi Jianxin ya kara da cewa, asusun raya Sin da Afirka asusu ne na zuba jari, kuma ana gudanar da harkokinsa ne a kasuwanni, amma ba samar da taimako kawai ba, dole ne a amfana da aikinsa, shi ya sa muke kokarin samun moriyar da ta dace, amma ba mai tsoka ba, wato irin ta zuba jari da zai samu dauwammamen ci gaba, dalilin da ya sa haka shi ne domin irin wannan zuba jarin zai dade yana amfanawa sassan biyu cikin kwanciyar hankali.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China