in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa ofishin asusun raya Sin da Afirka a Kenya
2016-09-23 11:00:20 cri

Jiya Alhamis an kafa ofishin asusun raya kasar Sin da kasashen Afirka a kasar Kenya a birnin Nairobi, hedkwatar kasar.

Ofishin asusun raya Sin da Afirka da aka kafa a Kenya ya kasance reshe na biyar ne da aka kafa a Afirka, kuma jakadan kasar Sin dake kasar Kenya Liu Xianfa da shugaban asusun Chi Jianxin da ministan kudin kasar Kenya Henry Rotich da ministan dake kula da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da sufuri da gidajen kwana da harkar raya biranen kasar Kenya James Masharia sun halarci bikin tare da sauran wakilai kusan 150 da suka zo daga gwamnatin kasar Kenya da kamfanoni da hukumomin kasa da kasa dake wakilci a kasar.

Yayin bikin, shugaban asusun Chi Jianxin ya bayyana cewa, tun bayan da aka kafa asusun raya Sin da Afirka a watan Yunin shekarar 2007, wato a cikin shekaru 9 da suka gabata, asusun ya taka muhimmiyar rawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin sassan biyu, musamman ma a fannonin da ke shafar aikin gona da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a. Chi Jianxin ya ce, "Kawo yanzu, mun riga mun tsai da kuduri cewa, za mu zuba jari kan ayyuka guda 87 a kasashen Afirka 36, kuma an yi hasashe cewa, idan za a iyar aiwatar da wadannan ayyuka yadda ya kamata, kenan, za a kara adadin kudin da kasashen Afirka za su samu daga wajen fitar da kayayyaki zuwa ga kasashen waje a ko wace shekara har zuwa dalar Amurka biliyan 2, adadin harajin da za a samu kuwa zai karu da dalar Amurka sama da biliyan daya, lamarin da zai amfanawa al'ummun kasashen da yawansu zai kai miliyan daya."

Chi Jianxin ya ci gaba da cewa, dalilin da ya sa aka kafa ofishin asusun a Kenya shi ne domin kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya, har ma da kasashen dake gabashin Afirka baki daya. Yana mai cewa, "Cikin dogon lokaci, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan hadin gwiwa dake tsakaninta da Kenya, yanzu dai muna jin dadi da ganin gwamnatin Kenya tana kokarin shigo da jari daga kasashen waje ta hanyoyi daban daban, ko shakka babu asusun zai taka rawa wajen sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Kenya."

Yayin bikin, jakadan kasar Sin Liu Xianfa shi ma ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, a shekarar 2015, adadin cinikin dake tsakanin Sin da Kenya ya zarce dalar Amurka biliyan 6, wato ya karu bisa kashi 20 cikin dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2014, ana iya cewa, hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu yana da makoma mai haske. Liu Xianfa ya yi nuni da cewa, "Kenya tana da karfi a asirce wajen samun bunkasuwar tattalin arziki, kuma tana yin kokari matuka domin kara samun jarin waje, yanzu an kafa ofishin asusun a kasar, tabbas ne zai kara jawo hankalin 'yan kasuwar kasar Sin da su zuwa kasar ta Kenya domin zuba jari, kana hakan zai sa kaimi kan bunkasuwar masana'antu a Kenya da sauran kasashen gabashin Afirka, tare kuma da kara kyautata zaman rayuwar al'ummun Kenya. Kazalika, zumuncin gargajiya dake tsakanin Sin da Kenya zai kara zurfafa karkashin kokarin da sassan suke yi wajen zuba jari da kuma hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki."

Ministan kula da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da sufuri da gidajen kwana da harkar raya biranen kasar Kenya James Masharia ya bayyana cewa, kafuwar ofishin a Kenya zai kara jawo hankalin 'yan kasuwar kasar Sin domin su kara zuba jari a kasar ta Kenya, a madadin gwamnatin Kenya ne ya nuna godiya ga asusun saboda ya zabi Nairobin kasar Kenya da ya kasance wurin da aka kafa ofishinsa. Yana mai cewa, "Zaben da asusun raya Sin da Afirka ya yi ya nuna mana cewa, kasar Sin tana cike da imani kan hadin gwiwa dake tsakaninta da Kenya, shi ma ya bayyana cewa, Kenya tana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki a shiyyar gabashin Afirka."

Yayin bikin, asusun raya Sin da Afirka da hukumar zuba jari ta Kenya sun daddale wata jarjejeniya domin ingiza hadin gwiwa da zuba jari dake tsakanin sassan biyu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China