in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da taron zuba jari a kasashen ketare na Sin karo na 8
2016-09-21 11:07:01 cri

Za a kaddamar da dandalin hadin gwiwa kan samar kayayyaki tsakanin kasa da kasa karo na farko da taron zuba jari a kasashen ketare da kuma yin hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare na kasar Sin karo na 8 a nan birnin Beijing a ranar 20 ga watan Oktoban dake tafe. Taken taron da za a gudanar shi ne "Yin hadin gwiwa wajen samar da kayayyaki domin samun ci gaba tare". Kawo yanzu, an tabbatar da cewa, kasashe da yankuna sama da 80 za su halarci taron.

Taron zuba jari a kasashen ketare da kuma yin hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare muhimmin aiki ne da gwamnatin kasar Sin take yi domin samar da taimako ga kamfanonin kasar Sin domin su shiga kasuwar kasashen waje, an fara aikin nan ne kafin shekaru bakwai da suka gabata, ya zuwa yanzu, an riga an samu sakamako a bayyane, har ya samar da damammaki ga kasashen waje da su shigo da jari a kasar Sin.

An samu labari cewa, domin aiwatar da manufar kasar Sin ta shiga kasuwar kasashen duniya, da sa kaimi kan shirin "Ziri daya da hanya daya" da kuma hadin gwiwa wajen samar da kayayyaki dake tsakanin kasa da kasa, tun daga wannan taron da za a gudanar da shi a wata mai zuwa, za a gudanar da dandalin hadin gwiwa kan samar da kayayyaki dake tsakanin kasa da kasa yayin da ake gudanar da wannan taron, hadin gwiwar da za a kara karfafawa dake tsakanin kasar Sin da kasashen da abin ya shafa zai kumshe da fannoni 12, alal misali, layin dogo da lantarki da sarrafa-sarrafen albarkatun man fetur da mota da injuna da aikin sararin sama da jirgin ruwa da ayyuka kan teku da dai sauransu.

A yayin taron watsa labarai kan aikin share fagen da aka shirya a jiya Talata, shugaban kungiyar raya sha'anin kasar Sin a kasashen waje ta kasar Sin Hu Weiping ya yi mana bayani cewa, a wannan taron da za a gudanar da shi a wata mai zuwa, za a mayar da takensa kamar haka "Yin hadin gwiwa wajen samar da kayayyaki domin samun ci gaba tare", hakan ya nuna cewa, za a samu babban sakamako saboda taken nan ya fi dace da manufar kasar Sin. Hu Weiping ya ce, "Dandalin hadin gwiwa kan samar da kayayyaki dake tsakanin kasa da kasa zai kasance taro na farko da zai shafi dukkanin larduna da birane na fadin kasar Sin da kuma dukkannin manyan sana'o'i a kasar, har kuma taron zai samar da damammaki ga dukkanin kasashen duniya baki daya, yayin taron, za a tattauna muhimman manufofin da suka fi jawo hankulan al'ummun kasashen duniya, a saboda haka, jami'an gwamnatoci da 'yan kasuwa da masanan da abin ya shafa da suka zo daga kasar Sin da kasashen waje za su taru wuri daya domin yin shawarwari. "

Sabbin alkaluman da aka samu sun bayyana cewa, tun daga shekarar 2012, har zuwa yanzu, adadin jari iri ba na kudi ba da kasar Sin ta zuba a kasashen waje kai tsaye ya kasance matsayi na 3 a fadin duniya, kana adadin jarin da kasar Sin za ta zuba a kasashen waje ya kai matsayi na 9 a duniya.

Kazalika, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayyana cewa, tun daga watan Janairun bana, har zuwa watan Yulin bana, 'yan kasuwan kasar Sin sun zuba jari ga kamfanonin kasashen waje 5465 dake kasashe 156, gaba daya adadin jarin da suka zuba ya kai dalar Amurka biliyan 102.75, adadin ya karu ne bisa kashi 61.8 cikin dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara. Ana iya cewa, kokarin da kasar Sin take yi ya samar da guraben aikin yi da dama ga al'ummun kasashen duniya, hakan kuma ya taimaka matuka wajen ci gaban tattalin arzikin wadannan kasashe.

An ce, wakilai daga kasashe da yankuna sama da 80 kamar su Amurka da Canada da Rasha da Belgium da Hungary da sauransu za su halarci taron, kuma za su yi bayani kan muhallin zuba jari da sana'o'i na gari da ayyukan zuba jari na kasashensu.

Jami'in kasuwancin ofishin jakadancin kasar Hungary dake wakilci a kasar Sin Gabor Szekely wanda ya taba halartar irin wannan taro sau da dama ya bayyana cewa, irin wannan taron zai sa kaimi kan hadin gwiwa dake tsakanin sassa daban daban. Ya ce, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, adadin jarin da kasar Sin ta zuba a Hungary ya riga ya kai dalar Amurka biliyan 3.5, nan gaba kuma hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Hungary zai samu ci gaba yadda ya kamata, ina ganin cewa, taron zai samar da damammaki masu kyau ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Hungary, kana taron zai kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Hungary, har ma da kasashen dake tsakiya da kuma gabashin Turai baki daya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China