in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya bayyana matsayin Sin kan batun 'yan gudun hijira a taron MDD
2016-09-20 10:46:12 cri

Jiya Litinin 19 ga wata da safe, agogon wurin, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci babban taron da aka shirya musamman domin warware matsalar 'yan gudun hijira da makaurata a birnin New York, hedkwatar MDD, kuma ya yi jawabi a yayin taron, inda ya jaddada cewa, kasar Sin babbar kasa ce mai tasowa, shi ya sa tana son sauke nauyinta, kuma za ta dauki matakai a jere domin samar da taimakon jin kai ga mutanen dake cikin bukata.

Tun bayan farkon wannan shekarar da muke ciki, matsalar 'yan gudun hijira da makaurata ta fi jawo hankulan al'ummun kasashen duniya, ita ma ta kasance daya daga cikin manyan batutuwan da za a tattauna a yayin babban taron MDD karo na 71.

A cikin jawabin da ya yi a yayin wannan taron da aka shirya domin warware matsalar 'yan gudun hijira da makaurata, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, matsalar nan tana shafar zaman lafiya da ci gaban kasashen duniya, kana tana kawo tasiri ga zaman karkon shiyya shiyya, har ma za ta haifar matsaloli da dama a fannonin siyasa da tattalin arziki da zaman takewar al'umma da kuma kwanciyar hankali. Li Keqiang ya ce, "A halin da ake ciki yanzu, adadin 'yan gudun hijira da makaurata ya karu cikin sauri kuma bisa babban mataki, har ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru sama da goma da suka gabata, lamarin ba ma kawai ya kawo barazana ga ci gaban kasashen da abin ya shafa ba, har ma ya kai illa ga farfadowar tattalin arzikin kasashen duniya da tsarin kasa da kasa, ban da wannan kuma, matsalar 'yan gudun hijira da makaurata ita ma ta samar da mammunan tasiri ga karuwar hare-haren ta'addanci. Ana iya cewa, matsalar tana shafar moriyar ko wace kasa a fadin duniya, bai kamata ba a kasa magance wannan matsalar ba, wajibi ne ga kasashen duniya su dauki matakai tare domin dakile matsalar yadda ya kamata."

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, yayin da ake kokarin warware matsalar 'yan gudun hijira, kamata ya yi a mai da hankali kan hakikanin yanayin da kasashen da suke shirya samar da taimako ga 'yan gudun hijira suke ciki, haka kuma an gano babban tasirin da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD da sauran wasu kungiyoyin kula da makaurata na kasashen duniya, amma wajibi ne kuma kasashen da 'yan gudun hijira suka fito su ma su yi kokari bisa karfin kansu. Li Keqiang ya bayyana cewa, "Kasashen da suke shirya karbar 'yan gudun hijira suna daukar matakan da suka dace domin samar da taimako gare su, yanzu abu mafi muhimmanci shi ne a tattara isassun kudade da kayayyaki domin tabbatar da zaman rayuwar 'yan gudun hijira, ban da haka kuma kamata ya yi a kara kyautata ayyukan karbar makaurata, da haka za a yaki da laifufukan jigilar mutane da kuma ayyukan ta'addanci. Kazalika, idan ana son warware matsalar 'yan gudun hijira daga duk fannoni, wajibi ne kasashen da 'yan gudun hijira suka fito su yi iyakacin kokari da kansu. Kamar yadda aka sani, rikice-rikice da yake-yake da talauci su ne muhimman dalilan da suka haifar matsalar 'yan gudun hijira, a saboda haka, dole ne sassan da abin ya shafa su yi kokari matuka domin warware sabane-sabanen da ke tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari. Sauran kasashen duniya kuma kamata ya yi su shawo kansu domin cimma burin tabbatar da ci gaba da hadin kai da kwanciyar hankali a fadin duniya."

Li Keqiang ya jaddada cewa, bisa matsayinta na babbar kasa mai tasowa, kasar Sin tana son sauke nauyin dake bisa wuyanta da kanta domin ba da gudummuwa kan batun warware matsalar 'yan gudun hijira. Ya ce, "Har kullum kasar Sin tana mai da hankali sosai kan batun 'yan gudun hijira, kuma tana sanya kokari matuka domin warware matsalar, ko a baya lokacin da take fama fa da talauci, to, yanzu dai tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasuwa bisa babban mataki, amma ita kasa ce mai tasowa, tana son samar da taimakon jin kai gare su."

Li Keqiang ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta dauki matakai a jere domin samar da taimakon jin kai ga 'yan gudun hijirar da suka rasa muhallansu, kuma tana son yin hadin gwiwa dake tsakaninta da hukumomin kasa da kasa da kuma kasashe masu tasowa, domin warware matsalar 'yan gudun hijira da makaurata yadda ya kamata.

Wannan taron da aka shirya jiya karo na farko ne da aka tattauna batun dakile matsalar 'yan gudun hijira da makaurata a yayin babban taron MDD tun bayan da aka kafa MDD a shekerar 1945, yayin taron, an zartas da "sanarwar New York game da matsalar 'yan gudun hijira da makaurata," inda aka yi alkawari cewa, za a kare hakkin 'yan gudun hijira, kuma za a samar da goyon baya ga kasashen da za su karbar 'yan gudun hijira, tare kuma da kara samar da taimakon jin kai ga masu bukata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China