in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin tunawa da harin 9-11
2016-09-12 14:27:21 cri

A ranar 11 ga watan Satumba na ko wace shekara, a kan gudanar da bikin tunawa da mummunan harin ta'addancin da aka kai a Amurka shekaru 15 da suka wuce. A jiya Lahadi, a wajen baraguzan manyan gine-ginen World Trade Centre dake birnin New York na kasar Amurka, wadanda aka rusa ta hanyar harin ta'addanci a shekarar 2001, an gudanar da bikin tunawa da harin, inda mutanen da suka tsira da rayukansu, da iyalan wadanda suka rasa rayuka sakamakon harin, suka kira sunayen mutanen da suka mutu kusan dubu 3 daya bayan daya, don bayyana yadda ake begensu sosai. "da babana Jacob. Jikokinsa Mia, Gretchen, Grace, William da Lailey, ba su taba ganinka ba, kuma ba za su samu wannan dama ba har abada. Muna sonka, baba."

 A wurin da aka taba kai masa hari dake ginin Pentagon na birnin Washington, hedkwatar kasar Amurka, shugaban kasar Barack Obama ya bayyana a wajen wani taron gangami cewa, yanayin tsaron kasar ya canza. "Cikin shekaru 15 da suka wuce, barazanar da muke fuskanta ta canza. Yayin da muka kara karfin tsaron kai, 'yan ta'adda sun fara kai hari ga kananan wurare, duk da cewa harin na cigaba da sanadin rasa rayuka. Haka kuma suna kokarin nuna ra'ayi na kiyayya, da sanya karin mutane amfani da karfin tuwo, lamarin da ya haddasa karin wasu hare-hare a wurare daban daban."

Hakika a cikin jawabin da shugaba Obama ya yi ta gidan telabijin a ranar Asabar, ya ce yanayin tsaron Amurka yana da karfi sosai, wanda zai iya dakile barazanar harin ta'addanci makamancin na ranar 11 ga watan Satumba, idan ka samu yiwuwar sake bullowar wani harin. Sai dai wasu hare-haren ta'addanci da mutum guda zuwa biyu suka aikata, kamar fashewar bom a wurin wasan gudun fanfalaki na birnin Boston, da harin bindiga a San Bernardino na kasar Amurka, suna cigaba da faruwa a kai a kai, kuma da wuya a hana faruwar irinsu.

A cewar shugaban kasar Amurka, duk da cewa yanayin tsaron kasar ya canza sosai, amma tsarin al'ummar kasar na kunshe da 'yan kasashe daban daban da al'adu daban daban bai canza ba ko kadan, ganin wannan ya kasance tushen kafuwar kasar Amurka. Sai dai a wani bangaren na daban, wasu 'yan siyasa na kokarin janyo baraka ga kasar, ganin yadda ake samun sabanin ra'ayi sosai ta fuskar aikin tsaro tsakanin 'yan takarar neman shugabancin kasar. Donald Trump, dan takarar Jam'iyyar Republicans, ya bada shawarar cewa, ya kamata a hana Musulmai shiga cikin harabar kasar Amurka, bayan abkuwar harin ta'addanci a San Bernadino a karshen shekarar bara.

Kalaman nasa ya samu goyon baya daga wasu jama'ar kasar, duk da cewa masu sanin ya kamata da yawa na kasar sun yi suka inda suke cewa ra'ayinsa zai janyo baraka da kiyayya tsakanin al'ummomin kasar, tare da sanya kasar ta zama saniyar ware a duniya.

A wajen bikin tunawa da harin wanda ya gudana a birnin New York a jiya Lahadi, wata mace Bayahudiya wadda mijinta ya mutu sakamakon harin ta'addanci ta ce, ita da diyarta sun taba gamuwa da wani iyalin Musulmai, wadanda suka rasa wasu iyalansu a harin. A cewar Bayahudiya, zukatansu a tare suke, "Dukkanmu wani bangare ne na duniyarmu. Ba mu da wani matsayi da ya fi na wani, matukar halayyar musamman na kanmu. Akwai alaka sosai tsakaninmu."

Abin takaici shi ne, sabanin ra'ayin wannan Bayahudiya, 'yan siyasar kasar Amurka na kara kokarin janyo rabuwar al'ummar kasar gida 2. A ranar 9 ga wata, majalisar wakilan kasar da Jam'iyyar Republicans ke da rinjayen kujeru ta zartas da wata doka, don rufa ma iyalan wadanda suka mutu sakamakon harin ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumba baya, domin su kai kara ga gwamnatin kasar Saudiyya, ganin wasu 15 daga cikin 'yan ta'adda 19 da suka kai wannan hari 'yan kasar Saudiyya ne. Sai dai a nata bangare, fadar shugabancin kasar ta White House ta nuna cewa, shugaban kasar Barack Obama zai soke wannan doka bisa ikonsa na kin amincewa da wasu dokoki da ya ga ba su dace ba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China