in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana aiwatar da shirin "ziri daya da hanya daya" cikin sauri fiye da kima
2016-09-08 11:31:35 cri
Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 3 da fitar da shirin "ziri daya, hanya daya". A lokacin da ake kaddamar da wasu muhimman ayyuka a wasu yankuna da kasashe bisa shirin, ana aiwatar da shirin cikin sauri fiye da kima, kuma an riga an samu kyakkyawan sakamako da dama. Masana sun ce, kasar Sin da kasashe makwabta suna kokari tare, wajen aiwatar da shirin domin neman samun moriya cikin hadin gwiwa. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.

A ran 7 ga watan Satumba na shekarar 2013, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da wani muhimmin jawabi, a lokacin da ya kai ziyara a kasar Khazakstan, inda a karo na farko ya gabatar da muhimmiyar shawarar sake bunkasa "zirin tattalin arziki na Siliki". Mr. Xi Jinping ya bayyana cewa, "Ya kamata mu kirkiro sabon salon yin hadin gwiwa, wato za mu iya kafa 'zirin tattalin arziki na siliki' cikin hadin gwiwa, ta yadda za a iya kara yin hadin gwiwa a karin fanonni daban daban a tsakanin kasashen Turai da Asiya. Wannan shiri zai haifar da alheri ga jama'ar dake zaune a yankunan dake kusa da zirin."

Sannan bayan wata daya kacal, a lokacin da Mr. Xi ya kai ziyara a kasar Indonesia, ya gabatar da wani muhimmin jawabi a majalisar dokokin kasar, inda ya nuna cewa, kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa da kasashen Asean a yankunan teku wajen kafa "hanyar siliki ta teku ta karni na 21".

Wadannan shirye-shirye biyu da yanzu muke kiransu "ziri daya, hanya daya" a takaice, sun ratsa nahiyoyin Asiya da Turai, sun kuma shafi al'ummomi biliyan 4.4. Sannan yawan GDP da ake da su a kasashen da shirin ya shafa, ya kai dalar Amurka biliyan dubu 230. Manazarta suna ganin cewa, baya ga wannan shiri da gwamnatin kasar Sin ta tsara domin kafa sabon tsarin tattalin arziki dake bude kofa ga duk duniya, shirin zai kuma zamo "shirin kasar Sin" da zai iya ingiza aniyar kasashen duniya wajen inganta hadin gwiwa, su kuma samu nasara tare.

A yayin wani taron kara wa juna sani da aka shirya a kwanan baya, Mr. Wu Hongbo, mataimakin babban sakataren MDD ya yi sharhi cewa, "Ainihin ruhun shirin'ziri daya, hanya daya' shi ne kara yin hadin gwiwa domin samun nasara da ci gaba da wadata tare. Tunani na 'shimfida zaman lafiya da hadin gwiwa da bude kofa ga kasashen duniya da amincewa da juna, da kuma fahimtar juna, yana dacewa da ruhin adanjar neman ci gaba ba tare da tangarda ba nan da shekarar ta 2030."

Ya zuwa yanzu, yawan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da suke aiwatar da wannan shiri na "ziri daya, hanya daya" ya riga ya kai fiye da 100. Kasar Sin ta daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa na aiwatar da shirin da kasashe fiye da 30, sannan ta yi hadin gwiwa da kasashe fiye da 20 wajen bunkasa masana'antu da samar da makamashin halittu.

Bugu da kari, ya zuwa yanzu kimar asusun bunkasa masana'antu da samar da makamashi da aka kafa tsakanin bangarori daban daban, ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 100. Kamfanonin kasar Sin sun kafa shiyoyi na hadin gwiwa 46 a wasu kasashe. Mr. Andre Laboul, mataimakin daraktan sashen kula da harkokin hada-hadar kudi da masana'antu a kungiyar hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da ci gaba wato OECD, yana gani cewa, a lokacin da tattalin arzikin duniya ya yi rauni wajen samun karuwa yadda ya kamata, shirin "ziri daya, hanya daya" yana da muhimmanci matuka ga kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya. Mr. Andre ya bayyana cewa, "A ganina, yana da muhimmanci sosai wajen inganta hadin gwiwa, da mu'amala domin bunkasa tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta dauki jerin matakai. Alal misali shirin 'ziri daya, hanya daya' ba ya ga matukar muhimmanci da yake da shi ga tattalin arzikin shiyya-shiyya, yana kuma da tasiri a duk duniya baki daya. Kasar Sin ta samar da wata muhimmiyar alama ta fatan yin hadin gwiwa da mu'amala tsakanin yankunan shiyya-shiyya, da kuma duk duniya tare."

Bisa kididdigar da aka fitar, an ce, a shekarar 2015, yawan darajar kayayyakin da ake shige da ficen su a tsakanin kasar Sin da kasashe wadanda suke aiwatar da shirin, ya kai dalar Amurka kusan biliyan dubu 1, sannan yawan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a wadannan kasashe ya kai dalar Amurka biliyan 15, wato adadin ya karu da kashi 18 cikin dari bisa makamancin sa a shekarar 2014. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China