in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Qu Xing: Taron kolin G20 na Hangzhou zai yi babban tasiri ga yanayin tattalin arzikin duniya
2016-09-07 13:41:56 cri

A ranar Litinin 5 ga wata, aka rufe taron shugabannin kungiyar G20 a birnin Hangzhou da ke gabashin kasar Sin. A gun taron na yini daya da rabi, shugabanni mahalarta taron sun yi shawarwari bisa ga taken taron, da ma sauran muhimman batutuwa, tare kuma da cimma nasarori masu armashi. Kasancewarsa mashahurin masanin ilmin harkokin kasa da kasa, kana jakadan kasar Sin a kasar Belgium, Mr. Qu Xing ya mai da hankali sosai a kan taron, kuma a yayin da yake yin hira tare da wakilinmu a jiya, ya bayyana cewa, taron da aka gudanar a birnin Hangzhou ya kasance mafi kasaita kuma mafiya samun nasarori masu armashi, kuma mafi samun yawan kasashe mahalarta a tarihin kungiyar ta G20, kuma tabbas zai haifar da babban tasiri ga yanayin tattalin arzikin duniya.

Wani babban sakamakon da aka cimma a gun taron koli na Hangzhou shi ne zartas da shirin samun bunkasuwa bisa kirkire-kirkire na G20, inda ake sa ran yin kirkire-kirkire ta fannin kimiyya da fasaha, ta hakan kuma a raya kirkire-kirkire ta dukkanin fannonin da suka hada da ra'ayoyin al'umma da tsarurruka da ma sauransu, sa'an nan a ji dadin nasarorin da aka samu daga kirkire-kirkire. A ganin jakadan, samar da kirkire-kirkire a fannin hanyoyin samun bunkasuwa yana da muhimmanci matuka musamman sabo da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a duniya. Ya ce, "Ina ne bakin zaren warware wannan matsala? A da, a kan kara zuba jari, sai dai hakan na iya haifar da matsalar samar da kayayyaki fiye da kima, tare kuma da kashe albarkatu masu yawa, wanda kuma bai warware ainihin matsalar da ake fusknata ba. Don haka, kamata ya yi raya tattalin arziki bisa yin kirkire-kirkire, a yi kwaskwarima ta fannin samar da kayayyaki, a yayin da ake kiyaye bukatun kasuwanni, a kuma kara inganta fannin samar da kayayyaki. To, amma ta yaya za a cimma burin? Ya zama dole a yi kirkire-kirkire, kuma a tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki bisa kirkire-kirkire. A ganina, a gun taron koli na Hangzhou, an aika da wannan sako ga duk duniya, wanda kuma ya samu amincewa daga shugabannin kungiyar G20 da ma na sauran kungiyoyin duniya, don haka, wannan sakamako na da matukar muhimmanci, haka kuma ya kasance tamkar wani magani da kasar Sin ta samar musamman sabo da cutar da ke addabar tattalin arzikin duniya a halin yanzu."

A gun taron, an kuma yanke shawarar kyautata tsaron gudanar da harkokin hada-hadar kudi a duniya, don kara karfin tinkarar matsalolin tattalin arziki. Shugabanni mahalarta taron sun amince da sa kaimin yin kwaskwarima a kan kason kasa da kasa a cikin hukumomin kudi na duniya, tare da inganta matakan gyare-gyaren harkokin hada-hadar kudi, domin kiyaye kwanciyar hankali a kasuwannin hada-hadar kudi. A game da wannan, Mr. Qu Xing yana ganin cewa, tun bayan barkewar rikicin hada-hadar kudi a duniya a shekarar 2008, kowa na furucin yi wa tsarin hada-hadar kudi kwaskwarima, domin kason kasashe masu tasowa ya iya bayyana matsayinsu a duniya, sai dai ba a cimma tabbatar da hakan ba. A gun taro na wannan karo, an sake wannan furucin, tare kuma da samar da wasu hakikanan ma'aunai, abin da ke da ma'ana sosai ga kasashe masu tasowa, musamman ma kasar Sin. Mr. Qu Xing ya ce, "Kasashe masu tasowa ba su samu isashen wakilci ba, don haka a gun taron, an sake jaddada batun, inda kuma aka samar da wasu hakikanan abubuwan da za a cimma, don a kara warware batun wakilcin kasashe masu tasowa. A hakika, daidaita batun wakilcin kasashe masu tasowa shi ne kara wa kasashen ikon jefa kuri'a, kuma kasar Sin ce za ta kara samun ikon hakan daga cikin kasashe masu tasowa, abin da ke da muhimmanci sosai, musamman ta fannin kara wa kasar fada a ji wajen gudanar da harkokin hada-hadar kudi a duniya."

A ganin jakadan, wani muhimmin sakamako na daban da aka cimma a gun taron shi ne, sanya batun samun bunkasuwa a wani muhimmin matsayi, ya ce, "Matsaloli da yawa da ake fuskanta yanzu a duniya sun taso ne a sakamakon batun rashin samun ci gaba. Ina dalilin da ya sa ake fama da tashin hankali a sassan duniya da dama? Dalili shi ne sabo da al'ummar sassan ba sa jin dadin zaman rayuwarsu. A lokacin da al'umma ba ta iya biyan bukatun zaman rayuwarta ba, lalle, da wuya a samu kwanciyar hankali. Don haka, kasar Sin ta gabatar da batun samun bunkasuwa a matsayin wani babban batun da za a tattauna a gun taron, don sa kaimi ga kasashe mambobin kungiyar G20 da su dauki alkawari a game da wannan batu, wannan wani muhimmin sakamako ne, kuma dalili ne da ya sa aka samu amincewa daga kasa da kasa." (Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China