in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta sassauta ma'aunin shigowar jarin waje
2016-08-24 11:26:38 cri

Mataimakin ministan kasuwanci na Sin Wang Shouwen ya fayyace a jiya Talata cewa, kasar Sin za ta sassauta ma'aunin shigowar jarin waje.

Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta kafa kamfanonin jarin waje dubu 850, wadanda suka jawo jarin kasashen waje har dalar Amurka biliyan 1720, adadin da ya fi na sauran kasashe masu tasowa yawa a cikin shekaru 24 da suka gabata. Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Wang Shouwen ya bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a kwanan baya cewa, a cikin shekaru 30 da suka gabata, bayan da aka fara gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a Sin, yawan jarin waje da Sin ta jawo ya rika karuwa, kana an rika kyautata hanyoyin yin amfani da jarin waje. Mr. Wang ya bayyana cewa,

"Taron bunkasuwar cinikayya na MDD ya yi bincike wanda ya bayyana cewa, nan da shekaru 3 masu zuwa, kasar Sin za ta ci gaba da zama daya daga cikin kasashe mafi jawo jarin kasashen waje. Kwamitocin 'yan kasuwa na kasar Amurka da na kungiyar EU dake kasar Sin, da hukumar inganta zuba jari na kasashen Sin da Japan sun yi bincike wanda ya nuna galibin kamfanonin da suka yi bincike a kansu, suna sa ran ganin kara samun ci gaba a kasuwannin kasar Sin."

Wang Shouwen ya gabatar da cewa, kamfanonin jarin waje sun samar da gudunmowa ga rabin yawan cinikayya a tsakanin Sin da kasashen waje, suna kuma samar da kashi 1 cikin 4 na duk yawan kudin da aka samu a sana'ar masana'antu a Sin, kana yawan harajin da suka biya ya dauki kashi 1 cikin 5 na duk yawansu da gwamnatin Sin ta samu, ban da haka kuma, sun samar da kashi 1 cikin 7 na duk yawan guraban ayyukan yi, a halin yanzu, kamfanonin jarin waje sun zama muhimmin kashi na tattalin arzikin Sin.

Hazalika, Mr. Wang ya bayyana cewa, Sin na fuskantar kalubale a fannin jawo jarin waje a wannan shekara. Tun daga watan Janairu zuwa watan Yuli na wannan shekara, an kafa sabbin kamfanonin jarin waje dubu 16 a Sin, adadin da ya karu da kashi 9.7 cikin dari bisa makamancin lokacin bara. Amma a watan Yuli, wannan adadi ya samu raguwa.

A nan gaba, kasashen duniya za su yi gasar jawo jarin waje mai zafi. Kasar Sin za ta ci gaba da sassauta abubuwan da aka kayyade wajen shigar da jarin waje, da kara kafa yankunan gudanar da cinikayya cikin 'yanci.

"Za mu ci gaba da sassauta manufofin kayyade shigowar jarin waje, musamman ma a fannonin tarbiyya da al'adu da hada hadar kudi da zuba jari a waje, za mu ci gaba da nazari kan sana'ar kera kayayyaki, domin kara shigo da jarin waje a kan wannan sana'a. Mun samu sakamako mai kyau wajen kafa yankunan gudanar da cinikayya cikin 'yanci, muna shirya gudanar da wannan manufa a duk fadin kasar Sin, haka nan Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje. Ban da haka kuma, za mu gaggauta gyara tsarin kulawa da jarin da 'yan kasuwa na kasashen waje suka zuba wa Sin."

A yayin da Sin ke kara jawo jarin kasashen waje, yawan jarin da Sin ta zuba wa kasashen waje ya rika karuwa cikin sauri, wanda ya fi yawan jarin da Sin ta samu daga kasashen waje, shi ya sa, yanzu Sin ta zama kasa mafi yawan zuba jari ga kasashen waje.

A matsayin bikin baje koli daya kadai na inganta zuba jari tsakanin Sin da kasashen waje, za a yi taron zuba jari karo na 19 daga ranar 8 zuwa ranar 11 ga watan Satumba a birnin Xiamen. Mataimakin shugaban lardin Fujian Liang Jianyong ya gabatar da cewa, fadin wurin yin taron zai kai muraba'in mita dubu 138, kuma taron zai kunshi shagunan nune-nune dubu 6, wanda zai zama mafi girma a tarihin gudanar da bikin. Mr. Liang ya bayyana cewa,

"Bikin zai kunshi dakunan musamman na batun zuba jari da jawo jari da kuma cinikayyar kayayyaki. Ya zuwa yanzu, 'yan kasuwan kasashen waje sun nuna sha'awa ga wannan biki sosai, inda hukumomi da yawa da suka fito daga kasashen Rasha da Japan da Saudiyya da Brazil da kuma sauran kasashe da yankuna fiye da 50 sun tabbatar da niyyarsu ta zuwan halartar bikin."(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China