in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe gasar wasannin Olympics ta birnin Rio
2016-08-22 11:02:23 cri

'Yan wasa kimanin dubu 11 da 400 daga kasashe da yankuna 206, da 'yan jarida dubu 25, da masu yawon shakatawa sama da miliyan daya ne suka shiga gasar wasannin Olympics a wannan karo a birnin Rio, hakan ya bayyana hakikanin yadda birnin Rio yake ga duniya baki daya. Yanzu haka dai an rufe gasar Olympics ta birnin Rio, ga kuma cikakken bayani daga wakiliyarmu Fatima.

A cikin wakar Bossa Nova mai dadin ji, shahararriyar 'yar nuna kwalliya ta kasar Brazil, Gisele Bündchen ta kwaikwayi wata mace daga garin Ipanema kan dandalin nuna fasahohi, inda ta bude gasar wasannin Olympics ta Rio. To, ko mene ne ra'ayin baki daga kasashen duniya game da gasar Olympics ta Rio?

Fang Liang, wani 'dan jaridar kasar Sin ne, yana ganin cewa, abin da ya fi burge shi a Rio shi ne son baki. Ya ce,

"Abin da ya fi burge ni shi ne mutanen Rio suna son baki kwarai. Misali, kamfanin jirgin sama ya yi lattin kawo akwatin kaya na, shi ya sa ban same shi ba. A yayin da nake neman akwatin, kowane mutum jami'i na tambaya na taimaka min cikin gaggawa. Ko da ba su san komai game da kayan nawa ba, suna taimaka min wajen neman su. Hakan ya burge ni sosai."

Guo Jingjing, wata Basiniya ce mai yawon shakatawa a Brazil. Kafin zuwanta, tana damuwa sosai, amma bayan isowarta Brazil, sai damuwar ta ta kau, sabo da ni'imtattun wurare da son bakin jama'ar kasar. Ta ce,

"Kafin na isa Brazil, na dan yi bincike a yanar gizo, inda na sami labarai marasa kyau da yawa dangane da kasar. Amma bayan isowata, ni'imtattun wurare da son bakin jama'a sun burge ni sosai. Mutane suna rayuwa cikin yanayi mai kyau. A matsayin wata mace daga ketare, cikin sauki na saba da rayuwarsu, su na koya mini wasan kwallon kafa da na raga cikin yakini."

Babu wata gasar wasannin Olympics da aka taba gudanarwa ba tare da aukuwar wasu kalubale kamar yadda ta faru a gasar Rio ba, kamar kai hari kan motar kafofin yada labarai, da shirya dakunan 'yan wasa cikin mawuyacin hali, da yin amfani da tutocin kasashen waje cikin kuskure da dai sauransu. Amma ba komai, jama'ar Brazil sun shirya gasar wasannin Olympics ta Rio da ta burge mutane kwarai da gaske bisa sahihanci, da son baki da suka gwada mana.

Game da wannan gasar Olympics ta Rio, ko mene ne ra'ayin wadanda suka shirya gasar? Magajin garin birnin Rio ya bayyana cewa, zai baiwa gasar Olympics ta Rio maki 10. Yana ganin cewa, gudanar da gasar Olympics ba zai kauda duk matsaloli ba, amma zai kyautata birnin yadda ya kamata. Ya ce,

"Wannan gasar wasanni ta Olympics ta bayyana karfinmu ga duniya baki daya. Birnin Rio na da karfin gudanar da irin wannan gagarumar gasa. Ko da yake gudanar da gasar ba zai warware matsalolinmu duka ba, amma zai kawo canji kadan ga birnin, ta yadda Rio zai bunkasa yadda ya kamata."

A nasa bangare, shugaban kwamitin gasar Olympics ta duniya, mista Thomas Bach, ya nuna babban yabo ga gasar Olympics ta Rio. Yana ganin cewa, ko da yake birnin Rio, har ma kasar Brazil tana fuskantar manyan matsaloli, amma jama'ar kasar sun gudanar da gasa mai kyau bisa sahihanci da son baki. A sa'i daya, mista Bach ya jaddada cewa, gudanar da gasar Olympics na bukatar kamar kashe kudade da yawa, amma ya warware wasu matsaloli yadda ya kamata, kamar samar da guraben aikin yi da dama, da samar da yanayi mai kyau ga birnin Rio. Mista Bach ya ce,

"Kafa filayen wasan motsa jiki domin gudanar da gasar Olympics ta Rio, ya samar da guraben aikin yi sama da dubu 10. Tun da aka canza hedkwatar kasar Brazil daga birnin Rio zuwa Brasilia, ba a taba zuba jari kamar haka a birnin Rio ba, cikin shekaru sama da 10 da suka wuce. Don haka idan aka ci gaba da daukar irin wannan mataki a Rio, yaya birnin zai zamo?"

Gasar Olympics ba ta da alaka da siyasa, a maimakon haka, za ta kara hada kan jama'ar kasar. Shugaban kasar Brazil na wucin gadi, Michel Temer ya bayyana cewa, 

"Gasar Olympics ta sake hada kan jama'ar Brazil. Bai kamata a sake shiga yakin basasa a Brazil ba, wannan ba salon jama'ar kasar ba ne."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China