in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron dandalin tattaunawar diflomasiyya tsakanin al'ummar Sin da Afirka a Tanzaniya
2016-08-10 10:49:56 cri

Jiya Talata 9 ga wata ne, aka kaddamar da taron dandalin tattaunawar diflomasiyya tsakanin al'ummar kasashen Sin da Afirka a Dar es Salaam, hedkwatar mulkin kasar Tanzaniya, wanda kungiyar kula da harkokin diplomasiyya tsakanin al'ummar kasa da kasa ta kasar Sin, da kuma gidan rediyon kasar Sin CRI suka shirya cikin hadin gwiwa. Mahalarta taron dai sun tattauna sosai a karkashin taken taron, wato "hadin kai don samun nasara tare, da bunkasuwa cikin hadin gwiwa, a kokarin ciyar da dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka gaba daga dukkan fannoni". Wasu daga mahalarta taron sun bayyana kalubalen da ake fuskanta a wannan fanni ba tare da rufe komai ba, baya ga wasu kyawawan shawarwari da aka gudanar.

An kira taron dandalin tattaunawar diflomasiyya tsakanin al'ummar Sin da Afirka ne bisa makasudin aiwatar da sakamakon da aka cimma a yayin taron koli na Johannesburg, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC wanda ya gudana a shekarar bara, da sa kaimi ga kara fahimtar juna da sada zumunci a tsakanin Sin da Afirka, gami da samar da tasiri na hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.

A tsawon lokacin taron, akwai kananan tarurukan dandalin tattaunawa da suka gudana guda uku, wadanda suka shafi cudanyar al'adu, da hadin gwiwar kafofin watsa labarai a tsakanin Sin da Afirka, da cudanyar aikin inganta jin dadin jama'a tsakanin bangarorin biyu, kana da hadin gwiwar aikin kiwon lafiya, da cudanyar magungunan gargajiya tsakanin bangarorin biyu, wadanda suka samu halartar baki daga sassan siyasa. Sai kuma fannin inganta tattalin arziki, da kafofin watsa labarai, da ilmi, da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da suka fito daga kasashen Sin, da Tanzaniya, da Najeriya, da Afirka ta Kudu, da Habasha, da Namibiya, da kuma Kenya.

A yayin taron, tsohon wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka Liu Guijin, ya bayyana cewa, babu shakka hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da kuma cudanyar jama'a a tsakanin Sin da Afirka, sun samu babban ci gaba a halin yanzu, amma duk da haka, akwai gazawa a wannan fanni, wato a fannin rashin fahimtar juna sosai a tsakanin bangarorin biyu. Yana mai cewa,

"Idan Sin da Afirka su gaza sanya harsashi mai inganci ta fuskar al'ummunsu, to, hadin gwiwarsu zai fuskanci matsaloli da yawa. Don haka, ya kamata a dora muhimmnaci kan aikin diflomasiyya a tsakanin al'umma, da kuma kara cudanya a tsakanin jama'a. A wani bangare, ya ce, ya kamata gwamnatocin Sin da Afirka su tsara manufofin da suka dace, domin ba da taimako da goyon baya ga wannan aiki na diflomasiyyar al'umma. A dayan bangaren kuma, dukkan Sinawa, ba kawai jami'an gwamnati ba, har ma da kwararru da matasa, da masu aikin watsa labarai, da masu ba da taimako ga kasashen waje, kana da 'yan kasuwa, ya kamata su mayar da kansu a matsayin ginshikai cikin wannan aiki, da kuma gudanar da shi bisa kyakkyawar zuciya."

Ban da wannan kuma, Liu Guijin na ganin cewa, ya kamata a kyautata hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a fannin watsa labarai, wato duk bangarorin biyu sun rika musayar labaran juna yadda ya kamata. Ya kara da cewa,

"A ganina, akwai wata gazawa da ta kamata mu kyautata, wato har yanzu ba ma iya samun isassun kungiyoyin al'umma da ba na gwamnati ba, don haka ya kamata gwamnatocinmu su kara mana azama, da kuma ba su jagoranci. Idan kowa na iya gudanar da aikin diflomasiyyar al'umma yadda ya kamata, to, Afirka za ta iya kara fahimtar kasar Sin sosai, sannan Sin za ta iya kara fahimtar Afirka. Hakan ne kuma zai kara kyautata halin da muke ciki yanzu, duba da cewa, muna samun yawancin labaran juna ne ta kafofin watsa labarai na yammacin duniya, wadanda su kan jirkita ainihin abubuwa."

Bugu da kari, a yayin karamin taron tattaunawa kan cudanyar al'adu da hadin kan kafofin watsa labarai na Sin da Afirka, mataimakin shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI Hu Bangsheng, ya gabatar da jawabi, inda ya furta cewa, ko da yaushe Afirka na kasancewa muhimmin yanki da CRI ke mai da hankali a kai wajen watsa labaru, da kuma gudanar da aikin diflomasiyyar al'umma. A ganinsa, ya kamata kafofin watsa labarai na bangarorin biyu su hada gwiwa sosai, wajen gabatar da kansu ga duniya yadda ya kamata. Ya ce,

"A halin yanzu, bunkasuwar kafofin watsa labarai na Sin da Afirka ba ta kai ta kasashen Turai da Amurka ba. Don haka dole ne Sin da Afirka su inganta hadin gwiwarsu, wajen gabatar da ainihin batutuwan da suka shafe su cikin adalci, kuma daga dukkan fannoni ga dukkanin sassan duniya. A matsayinsu na kasashe masu tasowa, ya kamata su yi kokari tare don kyautata tsarin watsa labarai maras adalci na duniya na yanzu, ta yadda za a iya samar da labaran Afirka da Sin yadda ya kamata."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China