in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi liyafar murnar cika shekaru 89 da kafa rundunar sojan kasar Sin a Abuja
2016-07-29 08:27:32 cri

 

Ranar Alhamis 28 ga wata ne, ofishin jakadancin Sin dake Najeriya ya shirya liyafa a Abuja, domin murnar cika shekaru 89 da kafa rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin. Wakilinmu Murtala Zhang dauke da karin bayani.

Liyafar dai ta samu halartar manyan jami'an gwamnatin Najeriya, ciki har da ministan tsaron kasa Mansur Mohammed Dan Ali, da ministan harkokin sadarwa Adebayo Shittu, da kuma shugaban hukumar kula da shige da ficen jama'a ta immigration Muhammed Babandede.

Makasudin shirya wannan liyafa shi ne, murnar cika shekaru 89 da kafa rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin, da kuma bayyanawa 'yan Najeriya ci gaban da sojojin kasar Sin suka samu, da kuma manufofin tsaron kasa na Sin.

A wajen liyafar, nayi hira da Mansur Dan Ali, wanda shi ne ministan tsaron kasa na Najeriya. Ya bayyana irin ci gaban da rundunar sojojin kasar Najeriya ta samu, da kuma hadin-gwiwar Najeriya da China a fannin tsaro.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China