in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kara yawan kujeru biyu na kasashen Afirka na samun izinin shiga gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya
2016-07-27 20:13:22 cri
A kwanakin baya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gana da shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA Gianni Infantino, inda ya bayyana cewa, jama'ar tarayyar Nijeriya suna kaunar wasan kwallon kafa. A don haka ne ma gwamnatin kasar ke kokarin raya sha'anin wasan, da bada umurni ga hukumar wasan kwallon kafa ta kasar game da gabatar da shirin raya wasan, da nuna goyon baya ga hukumar FIFA wajen gudanar da kwaskwarima. A daya hannun kuma, gwamnatin Nageriya ta yi farin ciki da zabar babbar sakatariyar hukumar ta FIFA wadda kuma 'yar asalin nahiyar Afirka ce.

A nasa bangare, Infantino ya bayyana cewa, ana shirin kara yawan kungiyoyi mahalarta gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya ta shekarar 2016 daga 32 zuwa 40, inda nahiyar Afirka za ta kara samun sabbin kujerun gasar a kalla biyu. Najeriya dai kasa ce da take da kwarewa a fannin wasan kwallon kafa a nahiyar Afirka, don haka ya yi kira ga mahukuntan kasar da su inganta, tare da gina ababen more rayuwa a wannan fanni, don samar da gudummawa ga sha'anin raya wasan kwallon kafa a nahiyar Afirka, da ma dukkan duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China