in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari ya kaddamar da layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna
2016-07-27 10:59:09 cri


Ranar Talata 26 ga wata ne, aka fara zirga-zirgar jirgin kasa na fasinja wanda ya hada birnin Abuja da jihar Kaduna dake tarayyar Najeriya. Wakilinmu Murtala dauke da karin bayani.

Wannan layin dogo da ya hada Abuja da Kaduna, wani kamfanin kasar Sin ne mai suna CCECC wanda ya dauki nauyin gina shi. Akwai manyan shugabannin Najeriya da jami'an gwamnati wadanda suka halarci bikin kaddamar da layin dogon, ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari, kakakin majalisar dattawa Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilan kasa Alhaji Yakubu Dogara, da ministocin sufuri, da muhalli da kuma ministan babban birnin tarayya da sauransu.

A cikin jawabin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar, ya bayyana muhimmancin wannan layin dogo da aka shimfida tsakanin Abuja da Kaduna.

Ya ce, an fara shimfida hanyar jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna tun shekara ta 2009. Daga yau kuma za mu samarwa al'ummar kasar Najeriya wata hanyar jirgin kasa mai tsaro, mai sauri da kuma mai dadi. Babu shakka layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna zai kasance wata gada, wadda zata taimaka ga ci gaban masana'antu, aikin gona da sauran harkoki a wadannan gurare biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China