in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka na kokarin yin hadin gwiwa domin neman kyakkyawar makoma
2016-07-25 11:35:25 cri

A kwanan baya, an shirya taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar AU karo na 27 a Kigali, hedkwatar kasar Ruwanda. Game da batutuwa iri iri da suke jawo hankulansu tare, kamar su halin tsaro da ake ciki a nahiyar, da aikin dinkewar dukkan kasashen Afirka, shugabannin kasashe mambobin kungiyar wadanda suka halarci taron sun yi kokarin cimma matsaya guda domin neman ci gaba tare cikin hadin gwiwa, kuma suna tsayawa tsayin daka kan matsayin neman ci gaba cikin lumana. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi ya hada mana.

Har yanzu ba a iya jin dadin halin tsaro da ake ciki a kasashen Afirka ba. Kungiyar Boko Haram ta tarayyar Najeriya, da ta al-Shabab ta Somaliya suna ta da zaune tsaye da kuma hallaka fararen hula. Sannan kuma, har yanzu ba a kawar da matsalolin da suka dade suna kasancewa a wasu kasashe ba. Sakamakon haka, a kan gamu da rikice-rikicen nuna karfin tuwo. A yayin taron, shugaban wannan zagaye na kungiyar AU, kuma shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya nuna kai tsaye cewa, halin tsaro mai tsanani sosai da ake ciki a kasashen Sudan ta kudu, da Burundi ya bayyana cewa, ana cike da kalubaloli iri iri a kan hanyar neman wata kyakkyawar makomar Afirka.

A yayin taron, shugabannin kasashe mambobin AU sun sa niyyarsu ta yin hadin gwiwa wajen dakile barazanar da ake kawowa kasashensu. Game da rikice-rikicen da ake yi a kasashen Sudan ta kudu, da Burundi da ayyukan ta'addanci da ake fuskanta a wasu kasashen Afirka, shugabannin sun tsai da kudurori, inda suka bayyana cewa, za a ci gaba da daukar matakan a zo a gani, ciki har da kafuwar asusun musamman na yaki da ta'ddanci, domin kokarin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka.

Bugu da kari, abin da ya fi jawo hankalin mutane a yayin taron shi ne fitar da fasfo na zamani na bai daya na Afirka, wato wani muhimmin aiki ne na "ajandar shekarar 2063", domin kokarin samun 'yancin zirga-zirgar kayayyaki da mutane a nahiyar. Yanzu shugabanni da ministocin harkokin waje na kasashen Afirka, da wakilansu dake zaune a hedkwatar kungiyar AU, sun riga sun samu wannan fasfo na zamani na bai daya na Afirka. A nan gaba, fararen hula ma za su samu irin wannan fasfo na zamani na bai daya na Afirka. Kasashen Afirka sun dauki matakan a zo a gani a kokarin dinkewar dukkan kasashen Afirka bai daya.

Nahiyar Afirka ta yanzu, wadda take neman kafa tsarin masana'antu na zamani, tana kokarin neman dauwamammen ci gaba bisa kanta, kuma daya daga cikin nahiyoyin da suka fi samun saurin ci gaban tattalin arzikinta. A ganin kasashe mambobin kungiyar AU, idan ana son dinkulewar dukkan kasashen Afirka bai daya, ba a iya rasa kowace kasar Afirka ba.

A waje daya kuma, kasashe mambobin kungiyar AU sun bayyana wani ra'ayi na bai daya, wato kasashen Afirka suna bukatar abokan hadin gwiwa, kamar kasar Sin a lokacin da suke neman ci gaba. A yayin taron koli na dandanlin tattaunawar hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka da aka shirya a birnin Johnnesberg na kasar Afirka ta kudu a watan Disamba na bara, an bude wani sabon shafin kara yin hadin gwiwa, domin neman nasara da ci gaba tare tsakanin kasashen Sin da Afirka. A cikin shekaru 15 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka, sun samu dimbin sakamako na a zo a gani, wadanda suke bayyana yadda kasar Sin take taka rawa a lokacin da kasashen Afirka suke neman ci gaba.

Mr. Erastus Mwencha, mataimakin shugabar kwamitin kungiyar AU ya ce, kasar Sin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ce ta kasashen Afirka, wadanda suka samu moriya sosai sabo da hadin gwiwar su da kasar Sin a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da kiwon lafiya da kuma tsaro. Ya kara da cewa, kasashen Afirka da Sin za su kara yin hadin gwiwa a fannoni uku, wato bunkasa masana'antu, da samar da ayyukan more rayuwar jama'a, da kawar da talauci a kasashen Afirka. Yanzu haka ana aiwatar da wasu shirye-shiryen. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China