in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin ta kira taro don tuna da zagayowar shekaru 10 da zartas da yarjejeniyar hakkin nakasassu a MDD
2016-07-08 11:37:52 cri

A jiya Alhamis, kwamitin nakasassu na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira taron tunawa da zagayowar shekaru 10 da zartas da yarjejeniyar hakkin nakasassu a MDD. Dan majalisar gudanarwa ta Sin kuma darektan kwamitin nakasassu na majalisar gudanarwa Wang Yong da babban sakataren MDD Ban Ki-Moon sun halarci taron.

Wang Yong ya yi jawabi cewa, yarjejeniyar hakkin nakasassu ta MDD ita ce yarjejeniya ta farko wajen kare ikon nakasassu daga dukkan fannoni a duniya. Gwamnatin kasar Sin ta gudanar da wannan yarjejeniya da kyau. A cikin shekaru 10 da suka gabata, gwamnatin Sin ta bi ka'idojin yarjejeniyar tare da kokarin kiyaye hakkin nakasassu yadda ya kamata.

Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya yaba wa gudummawar da kasar Sin ta yi wajen tsara da kuma gudanar da yarjejeniyar. Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 bayan da aka zartas da ita, wannan yarjejeniya ta taka muhimmiyar rawa wajen kyautata yanayin zaman al'umma ga nakasassu. Yawan nakasassu na kasar Sin ya ragu sosai, kasar ta kuma fitar da jerin ka'idojin raya ayyuka maras shinge domin kare hakkin nakasassu. Irin wadannan ayyuka sun aza harsashi mai kyau wajen daga matsayin nakasassu a zaman al'umma.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China