in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Rio ya yi imani da matakan kiyaye tsaro da za a dauka a yayin gasar
2016-07-07 17:05:59 cri
A kwanakin baya ne, kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na Rio ya gudanar da taron manema labaru, inda ma'aikatar shari'a ta kasar Brazil ta yi bayani game da yanayin matakan tsaron da aka tanada a wannan lokaci.

Ganin yadda ake fuskantar karuwar ayyukan ta'addanci a duniya, wannan lamari ya janyo hankulan kasashen duniya kan ko kasar Brazil tana da karfin tinkarar wannan matsala a yayin gasar wasannin Olympics ta Rio.

Haka zalika bama-baman da suka fashe a filin jiragen saman birnin Istanbul dake kasar Turkiya,ya kara janyo hankula 'yan jaridu game da yadda za a tinkari barazanar ta'addanci a yayin gasar wasannin Olympics ta Rio. Game da wannan, ministan sashen kula da harkokin tsaro a lokacin bukukuwa da ke hukumar shari'a ta kasar Brazil Andrei Rodrigues ya bayyana cewa, kasar Brazil tana daukar matakai don magance hare-haren ta'addanci. Ya ce, a fannin yaki da ta'addanci, kasar Brazil ta riga ta dauki dukkan matakan da suka dace.

Matakan tsaron da kasar ta dauka ba za su canja ba a sakamakon bama-baman da suka fashe a Istanbul, amma kasar za ta kara sa lura tare da yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashen duniya a wannan fanni.

A kokarin da ake yi na ganin an magance faruwar ayyukan ta'addanci a yayin gasar wasannin Olympics, sashen kiyaye tsaro a lokacin bukukuwa na hukumar shari'a ta kasar Brazil da rundunar 'yan sandan kasar Brazil sun kafa cibiyar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci, kana sun hada kai da hukumomin kasashen wajen da abin ya shafa. Ya zuwa yanzu, kasashe 7 ciki har da Amurka, Birtaniya, Faransa da sauransu sun tabbatar da yin hadin gwiwa tare da kasar Brazil wajen yaki da ta'addanci a wannan karo. Kana cibiyar hadin gwiwar 'yan sanda da aka kafa a yayin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2013 da gasar cin kafin duniya ta shekarar 2014 za ta ci gaba da taka rawa a yayin gasar wasannin Olympics ta Rio, 'yan sanda kimanin 250 daga kasashe 55 za su hada kai da 'yan sandan kasar Brazil wajen tattara muhimman bayanai da sakonni.

Wani muhimmin batun dake shafar kiyaye tsaro a yayin gasar wasannin Olympics ta Rio da aka nuna shakka a kai, shi ne raguwar kasafin kudi a wannan fanni. A ranar 17 ga watan Yuni ne, gwamnatin jihar Rio ta sanar da cewa, tana fama da matsalar karancin kudi, mukaddashin gwamnan jihar ya sanar da cewa, wannan na iya kawo nakasu ga aikin kiyaye tsaro a yayin gasar wasannin Olympics ta Rio.

Da yake mayar da martani kan wannan batu, Mr Rodrigues ya bayyana cewa, ba a rage kasafin kudi a fannin samar da tsaro ba, yana mai cewa, gwamnatin kasar ta yi alkawarin samar da kudin Brazil Real miliyan 290, don magance matsalar karancin kudi da gwamnatin jihar Rio take fuskanta. Kuma ministan harkokin shari'a na kasar ya bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta tabbatar cewa, an samar da wadannan kudade ga gwamnatin jihar a cikin wannan mako.

Ana sa ran cewa, kasar Brazil za ta tura sojoji da 'yan sanda da yawansu ya kai dubu 85 don tabbatar da tsaro a yayin gasar wasannin Olympics ta Rio. Mr Rodrigues ya jaddada cewa, kasar Brazil za ta yi kokarin ganin an tabbatar da tsaro, don haka 'yan wasa da masu yawon shakatawa su kwantar da hankalinsu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China