in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi maraba da shigar Sin cikin IOM
2016-07-01 10:11:08 cri

A ranar Alhamis, sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, ya yi maraba da shigar kasar Sin a cikin kungiyar hijira ta duniya (IOM), tare da bayyana cewa, kasar Sin za ta kawo babbar gudunmuwa a cikin wannan kungiyar.

Ganin cewa Sin ta zama mamba ta IOM, hakan na da tasiri sosai a wannan lokaci mai muhimmaci da ake ciki, inda batun 'yan gudun hijira da bakin haure yake bukatar mu kara mai da hankali a kai, in ji mista Ban a cikin wata sanarwa.

A farkon wannan wata, Sin ta gabatar da takardar neman shiga IOM, dake cibiya a birnin Geneva. A ranar Alhamis, kungiyar ta amince da wannan bukata ta kasar Sin.

Tun lokacin da kasar Sin ta zama mamba mai sanya ido a IOM a shekarar 2001, bangarorin biyu sun yi aiki tare yadda ya kamata domin karfafa karfi a fannonin kula da hijira da kuma kare kananan jakadu a ketare, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Lu Kang.

Da zaran kasar Sin ta shiga IOM, za ta taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin hijirar kasa da kasa, kana kuma za ta taimaka wajen karfafa dangantakar kasa da kasa a fannin hijira, in ji Lu Kang. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China