in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a birnin Istanbul na kasar Turkiya
2016-06-29 19:04:00 cri

A jiya da dare ne aka kai wani harin kunar bakin wake na ta'addanci a filin saukar jiragen saman Ataturk na birnin Istanbul da ke kasar Turkiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

A yau Laraba kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi matukar Allah wadai da wannan hari. Mr. Hong ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta yi adawa da duk wani nau'i na ta'addanci, a don haka ya yi kira ga kasashen duniya da su kara cimma daidaito da yin hadin gwiwa a fannin yaki da ta'addanci, domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya aikawa takwaransa na kasar Turkiyya Ahmet Davutoglu sakon jaje sakamakon wannan hari.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China