in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mambobin bankin AIIB zai karu zuwa kimanin 90
2016-06-29 13:33:27 cri

A jiya Talata ne aka kammala taron dandalin tattaunawar Davos na lokacin zafi na shekarar 2016 a birnin Tianjing da ke nan kasar Sin, inda mista Jin Liqun, shugaban bankin zuba jari ga kayayyakin more rayuwar jama'a na nahiyar Asiya AIIB, ya bayyana burin banki na samun karin mambobi, wadanda adadinsu zai kai kimanin 90 a farkon shekara mai zuwa.

Shawarar da kasar Sin ta gabatar na kara bunkasa shirin nan na 'Zirin Tattalin Arziki na Hanyar Siliki, da Hanyar Siliki ta Teku na Karni na 21', wato manufar 'Ziri daya da Hanya daya' a takaice, tana ta samun karbuwa daga kasashe masu ruwa da tsaki. Sa'an nan, a matsayin wani bangare na manufar shirin nan na 'Ziri daya da Hanya daya', bankin zuba jari ga aikin gina kayayyakin more rayuwa a nahiyar Asiya AIIB, wanda aka kafa bisa kiran da kasar Sin ta yi, yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata, inda ya zuwa yanzu aka zartas da ayyuka guda 4, gami da ba da rancen da ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 500.

Sai dai a yayin taron dandalin tattaunawar mai taken ' Aiwatar da manufar Ziri daya da Hanya daya don amfanawa bangarori daban daban', wanda ya gudana karkashin laimar dandalin tattaunawar Davos na wannan karo, shugaban bankin AIIB mista Jin Liqun ya bayyana niyyar bankin na samun karin mambobi.

"Yanzu haka akwai kasashe kimanin 30 da ke son zama mambobin bankin AIIB, don haka yawan mambobinmu zai kai 90 a farkon shekara mai zuwa. Zuwa lokacin, za mu samu karin wakilci a duniya. Wannan ya sa za mu kula da ayyuka masu alaka da manufar Ziri daya da Hanya daya, gami da ayyukan kasashen da ke da nisa da mu."

A cewar shugaban bankin na AIIB, yayin da ake zaben ayyukan da bankin zai saka jari ciki, za a bukaci ayyukan su cika wasu sharuda 3, Na farko su kasance masu samar da riba, biyan bukatun kare muhalli, gami da samun amincewar yawancin mambobin bankin kan ayyukan. Dangane da batun, shugaban bankin ya ce,

"Bisa tsare-tsaren shirin Ziri daya da Hanya daya da aka gabatar, ana iya ganin moriyar da shirin zai kawowa kasashe masu alaka da shi. Yanzu bankinmu zai gudanar da aikinsa ne sannu a hankali, kuma zai mai da hankali kan samun daidaito tsakanin yankuna da kasashe daban daban. Yayin da muke saka jari, za kuma mu duba ko ayyukan za su amfanawa kasashen da batun ya shafa."

A yayin dandalin tattaunawar da ya gudana, 'yan kasuwa da masu masana'antu na kasashe daban daban sun yi musayar ra'ayi kan fasahohin da aka koya wajen aiwatar da shirin Ziri daya da Hanya daya, inda yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na Teda-Suez da kamfanin zuba jari na Teda dake birnin Tianjing na kasar Sin ya kafa a kasar Masar, ya zama wani abin koyi ga mutanen da suka halarci taron, ganin yadda ta wannan hanya aka samar da kudin shiga da guraben aikin yi ga 'yan kasar Masar. Shugaban kamfanin Teda, mista Zhang Binjun, ya bayyana ra'ayinsa dangane da dalilin da ya sa kasar Sin take kokarin gudanar da shirin Ziri daya da Hanya daya, a cewarsa,

"Ba ma kokarin tallata masana'antu fiye da kima a nan kasar Sin. Idan ba a manta ba, daga shekarun 1980 zuwa 1990 yadda kasashe masu sukuni na Turai, da Amurka, da Japan suka yi kokarin sauya fasahar masana'antunsu. A lokacin sun sauya tsare-tsarensu, inda suke mayar da wasu masana'antu zuwa wasu kasashe. A daidai lokacin ne kuma kasar Sin ta fara bude kofa ka sauran kasashen duniya, inda ta karbi masana'antun da aka tuso keyarsu zuwa kasar, kana ta yi amfani da naurori, da fasahohin dake tare da su, sa'an nan ta kara kirkiro sabbin fasahohi. Bisa wannan dalili ne, aka sanya kasar Sin zama kasar da take fitar da kayayyaki masu yawa zuwa ketare."

Sa'an nan a nasa bangaren, shugaban rukunin kamfanonin kula da albaraktu mai suna Eurasian Resources Group, Benedikt Sobotka, ya ba da shawarar cewa, ya kamata a ba da karin kulawa ga yadda ake musayar ra'ayi a fannin al'adu, yayin da ake gudanar da shirin nan na Ziri daya da Hanya daya, ganin yadda shirin ya kasance wata dama mai kyau wadda za ta karfafa cudanyar al'ummomi, da ci gaban shiyyar da ake ciki.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China