in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masaniyar Zimbabwe ta ce, JKS ta taimakawa kasarta sosai wajen samun 'yancin kai da ci gaba
2016-06-28 13:32:56 cri

Bana shekaru 95 ke nan da kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, a cikin wadannan shekaru da suka gabata, ba kawai jam'iyyar ta kawo wa al'ummar kasar zaman wadata ba ne, har ma tana kokarin samar da taimako ga wasu kasashen dake karkashin danniyar mulkin mallaka domin su samun 'yancin kai, kana sakamakon da jam'iyyar ta samu wajen tafiyar da harkokin kasa,ita ma ta samar da abin koyi ga wadannan kasashe, kasar Zimbabwe tana daya daga cikinsu. Kwanan baya, Phyllis Johnson, shugabar cibiyar nazari kan huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake kudancin nahiyar Afirka ta amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi mata.

A jajibirin ranar cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wakilinmu ya shiga cibiyar nazari kan huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake kudancin Afirka da aka kafa a birnin Harare, fadar mulkin kasar Zimbabwe, shugabar cibiyar Phyllis Johnson mai nazarce kan huldar dake tsakanin Sin da kasashen kudancin Afirka cikin dogon lokaci, ta yi tsokaci game da zumuncin dake tsakanin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyar kawancen al'ummar kasar Zimbabwe mai mulki a kasar sosai. Phyllis ta bayyana cewa, "Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa yayin da kasar Zimbabwe ke kokarin neman 'yancin kai. Duk da cewa, al'ummar Zimbabwe ne suka nemi 'yancin kan kasar da kansu, amma sun cimma burinsu ne karkashin goyon bayan sauran kasashe, musamman ma daga kasar Sin. A shekarar 1963, masu aikin sa kai da dama na kasar sun je kasar Sin domin samun horaswar da aka yi musu, daga baya suka koma kasarsu suka amfani da sakamakon gwagwarmayar da suka koya a kasar Sin, a karshe dai suka cimma burin samun 'yancin kan kasar ta Zimbabwe."

A shekarun 1960, yayin da Zimbabwe ke kokarin neman samun 'yancin kai a kasar, kasar Sin ta taba samar da taimako ba tare da sharadi ba. Tun daga shekarar 1963, wasu shahararrun sojojin Zimbabwe na jam'iyyar kwawancen al'ummar kasar sun zo nan kasar Sin domin samun horaswa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta ba su taimakon makamai da dama. Phyllis Johnson tana ganin cewa, ba ma kawai wadannan sojoji sun koyi fasahar yaki daga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba ne, har sun koyi tunanin juyin-juya-hali daga wajen. Phyllis Johnson ta bayyana cewa, "Gaskiya horas da sojoji da samar da makamai suna da muhimmanci sosai ga kasarmu ta Zimbabwe, amma abu mafi muhimmanci shi ne sojojin sun yada tunanin juyin-juya-hali na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ga al'ummar kasar, hakan ya sa al'ummar Zimbabwe sun kara sanin me suke yi, misali, yakin sari-ka-noke, da kuma zumuncin dake tsakanin sojoji da fararen hula. A karshe dai, tunanin da suka koya a kasar Sin ya sauya hanyar yakin da suka yi, kuma sun yi nasara."

A shekarar 1980, Zimbabwe ta samu 'yancin kai karkashin jagorancin jam'iyyar kawancen al'ummar kasar, kasar Sin kuma ta kulla huldar diplomasiya da Zimbabwe a rana ta farko da aka samun 'yancin kai a kasar. A cikin shekaru 35 da suka gabata, kasashen biyu wato Sin da Zimbabwe sun yi kokarin taimakawa juna, zumuncin dake tsakaninsu ya kara zurfafa sannu a hankali. Ya zuwa karni na 21, shugaban jam'iyyar kawancen al'ummar kasar Zimbabwe kuma shugaban kasar Mugabe ya nuna kwazo da himma domin koyon manufar tafiyar da harkokin kasa ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Phyllis Johnson ta bayyana cewa, kasar Sin ta samu 'yancin kan siyasa karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, a shekarar 1978 kuma, ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, lamarin da ya kawo wa kasar ci gaban tattalin arziki. Phyllis Johnson tana mai cewa, "A fannin sauyawar tsarin tattalin arziki, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samar da sakamako da dama gare mu, ina ganin cewa, ya kamata Zimbabwe da sauran kasashen dake kudancin Afirka su kara mai da hankali kan masana'antu, kuma lokaci ya yi da za su kafa yankin musamman na tattalin arizki kamar yadda kasar Sin ta yi, yanzu dai kasar Sin ta riga ta samu babban ci gaba wajen bunkasuwar masana'antu, hakan ya nuna cewa, ya dace mu yi koyi da sakamakon da Sin ta samu."

Kana abu mafi ba ta mamaki shi ne babban sakamakon da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samu wajen tafiyar da harkokin kasa, ta ce, ya kamata kasar ta Zimbabwe ta koyi hanyar yin aiki ta jam'iyyar ta kwaminis ta kasar Sin wato ya fi kyau a kammala aikin cikin gajeren lokaci, ba tare da bata lokaci ba, misali gwamantin kasar Sin tana iya tsara shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin cikin makonni biyu kacal a yayin taron da aka saba gudanarwa a watan Maris na ko wace shekara.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China