in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ganin ya kamata a warware batun tekun kudancin Sin ta hanyar yin shawarwari
2016-06-27 11:54:55 cri

Jiya Lahadi, an gudanar da taron karawa juna sani game da batun yanke hukunci kan tekun kudancin kasar Sin da dokokin kasa da kasa a birnin Hague na kasar Holand, wasu kwararru da suka halarci taron suna ganin cewa, bai dace ba a warware batun tekun kudancin kasar Sin ta hanyar yanke hukunci, ko yin amfani da dokokin kasa da kasa, kamata ya yi kasashen da abin ya shafa su daidaita batun ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.

Cibiyar nazari kan dokokin kasa da kasa ta Grotius ta jami'ar Leiden ta kasar Holand, da cibiyar nazari kan iyakar kasa da harkar teku ta kasar Sin ta jami'ar Wuhan dake jihar Hubei ta kasar Sin ne suka shirya taron cikin hadin gwiwa. Kwararru sama da 30 da suka fito daga kasar Holand da Sin da sauran kasashe sun halarci taron, inda suka yi nazari da kuma tattaunawa kan batun game da yadda za a warware batun tekun kudancin kasar Sin.

Nico Schrijver, shehun malami a kwalejin koyar da ilmin dokoki na jami'ar Leiden ya bayyana cewa, makasudin shirya wannan taron karawa juna sani shi ne, domin samar da wani kyakkyawan muhalli ga kasashen da abin ya shafa saboda su yi hadin gwiwa a tsakaninsu, da kuma kara yin nazari da tattaunawa kan batun. Nico Schrijver, ya gayawa manema labarai cewa, a baya kasashen Turai sun taba samun sabani kan batun tafiyar da harkar teku ta arewa dake arewa maso yammacin nahiyar Turai, daga baya kasashen da abin ya shafa suka yi tattaunawa kuma suka daddale wata yarjejeniya, har suka warware sabanin lami lafiya. Nico Schrijver ya bayyana cewa, "Tekun yana da muhimmanci sosai gare mu, saboda yana taka muhimmiyar rawa wajen jigilar kayayyaki da ciniki da yawon bude ido da kuma kiyaye muhalli, shi ya sa wajibi ne mu yi hadin gwiwa da kasashen dake makwabtaka da kasarmu. A bisa tarihi, kasar Sin tana da halayyar daidaita kowace matsala cikin lumana, a saboda haka muna san koyon sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin, a sa'i daya kuma, muna son yin bayani kan sakamakon da kasashen Turai suka samu wajen daidaita matsalar teku ta arewa da kuma harkokin da ke shafar tekun Atlantik ga kasar Sin."

Mai taimakawa shugaban ofishin nazari kan dokokin kasa da kasa ta cibiyar yin nazarin kimiyyar zamantakewar al'ummar kasar Sin Liu Huawen ya gaya mana cewa, bisa alkaluman da aka samu, an ce, a halin da ake ciki yanzu, adadin rigingimu game da harkokin teku ya zarta 400, wadanda a ciki, an riga an warware kusan 100 daga cikin su, kuma an warware yawancinsu ne ta hanyar yin shawarwari, amma ba ta hanyar yin amfani da dokar kasa da kasa ba, dalilin da ya sa haka shi ne domin kawo yanzu ba a samu ra'ayi koda daya ba kan dokar. Liu Huawen ya jaddada cewa, akwai wuya a yi amfani da dokar teku yayin da ake daidaita matsalar dake shafar harkar teku. Yana mai cewa, "An daddale yarjejeniyar dokar teku ta MDD ne a shekarar 1982, bai dace ba a yi amfani da yarjejeniyar wajen warware daukacin matsalolin dake shafar harkar teku, kuma batu game da tekun kudancin kasar Sin shi ne sabanin dake da nasaba da hakkin tarihi, wanda kuma ya kasance tun kafin a daddale yarjejeniyar ta MDD, a saboda haka, bai dace ba a daidaita batun tekun kudancin Sin da yarjejeniyar kawai."

Tun bayan da kasar Philipines ta gabatar da kara kan batun a ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2013, sai karar ta jawo hankalin jama'ar kasashen duniya sosai, dalilin da ya sa haka shi ne kasar Amurka tana son yin amfani da batun domin hana bunkasuwar kasar Sin.

Shehun malamin kwalejin dokoki ta jami'ar Utrecht ta Holand Tom Zwart yana ganin cewa, akwai hadari a cimma burin siyasa ta hanyar yin amfani da dokokin kasa da kasa. Ya ce, "Hakan zai lahanta dokokin kasa da kasa, mun ga wasu kasashe, musamman ma wasu kasashen yamma ba su nuna halin dattaku ga kasar Sin, har wasu suna son sarrafa kasar Sin ta hanyar yin amfani da dokokin kasa da kasa, Amurka ta riga ta nuna irin wannan makarkashiyarta a fili. Ina ganin cewa, hakan zai kawo illa ga dokokin kasa da kasa da kuma huldar dake tsakanin shiyya-shiyya."

Tom Zwart ya jaddada cewa, kasashen Asiya sun fi son zaman jituwa, shi ya sa ba zai yiyu ba karar Philipines ta samu goyon baya a yankin, shi ma ya sake bayyana cewa, ya fi kyau a daidaita batun tekun kudancin Sin ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China