in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya sake jaddada goyon bayansa ga yarjejeniyar zaman lafiya a Mali
2016-06-22 10:42:43 cri

A albarkacin bikin tunawa yarjejeniyar zaman lafiya da sasanta 'yan kasar Mali karo na farko, babban sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, ya sake jaddada a ranar Litinin goyon bayan MDD kan wannan yarjejeniyar zaman lafiya.

A ranar 15 ga watan Mayun shekarar 2015, bisa rashin halartar kawancen 'yan tawayen Mali, kawancen kungiyoyin yankin Azawad (CMA) dake kunshe da manyan kungiyoyin 'yan tawaye uku dake arewacin Mali, gwamnatin Mali ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da sasantawa tare da mayakan sa kai dake goyon bayan gwamnatin Mali, har da wasu kananan kungiyoyin 'yan tawaye dake wannan kasa.

A ranar 20 ga watan Yuni, CMA ya rattaba kan wannan yarjejeniya a Bamako, babban birnin wannan kasa dake yammacin Afrika, domin kammala aikin rattaba hannu kan wannan yarjejeniya dake da manufar kawo karshen tashe tashen hankali tsakanin bangarori masu gaba da juna, da kuma aiwatar da tsare tsaren ci gaban yankin mai fama da rikici dake arewacin Mali, har ma da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar baki daya.

Karfafa aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali (MINUSMA) zai taimaka gwamnatin Mali wajen cimma burin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a cikin wannan kasa, in ji mista Ban. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China