in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD ya bukaci bangarorin Mali da su tabbatar da zaman lafiya a kasar
2016-06-17 12:58:48 cri

Jiya Alhamis manzon musamman na MDD dake kasar Mali ya bukaci bangarori daban daban na kasar Mali da su mayar da zaman lafiya da sansanta 'yan kasar Mali a cikin wannan kasa dake yammacin Afrika.

A wani jawabinsa a kwamitin sulhu na MDD, Mahamat Saleh Annadif, manzon musammun na sakatare janar na MDD kuma shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali (MINUSMA) ya bayyana cewa, shekara guda ke nan da gwamnatin Mali da kungiyoyi masu makamai sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Tun a shekarar 2012, kasar Mali ta fada cikin rikici da zaman dar dar a yankin arewacin kasar.

Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, da yake gabatar da rahoto kan muhimman sabbin abubuwan da suka faru a kasar Mali tun karshen watan Maris, manzon musammun na MDD ya nuna cewa, duk da cewa yarjejeniyar tana kunshe da kome, tun lokacin, shirin an maida shi kawai kan shawarwarin kan kafa wata hukumar wucin gadi, da ke tafiyar hawainiya wajen aiwatarwa.

Amma duk da haka, ya bayyana gamsuwa kan yarjejeniyar da aka cimma a wannan mako, a dabra da zaman taro karo na tara na kwamitin dake sanya ido kan yarjejeniyar. MINUSMA na tsayawa kan niyyarta kuma a shirya take wajen amfani da taimakonta domin tallafawa wajen kafa hukumomin wucin gadi nan take. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China