in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan kwallon Uganda sun isa Zimbabwe domin wasan sada zumunta
2016-06-01 17:47:17 cri
Kungiyar kwallon kafar kasar Uganda wadda ake wa lakabi da Uganda Cranes, ta isa kasar Zimbabwe domin buga wasan sada zumunci, a wani mataki na share fagen tunkarar wasan su na neman gurbin buga gasar nahiyar Afirka ta AFCON. Uganda dai za ta buga wasan neman gurbin ne da Botswana a ranar 4 ga watan Yuni.

Cikin sabbin yan wasan kasar na bana akwai dan wasan gaba Lorenzen Melvyn, wanda ke buga wa kungiyar Werder Bremen ta Jamus kwallo, ya kuma bayyana farin cikin sa game da samun damar bugawa babbar kungiyar kasar sa wasa a karon farko.

Uganda na matsayi na biyu a rukunin D da maki 7, inda take biye da Burkina Faso, wadda ta doke Uganda da ci daya da nema, a wasan su da ya gabata.

Yanzu haka dai Uganda na bukatar lashe wasannin ta biyu da za ta buga da Botswana da Comoros, kafin ta samu gurbin buga gasar nahiyar Afirka ta AFCON wadda za a gudanar badi a kasar Gabon.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China