in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid ta yi kasaitaccen bikin daukar kofi
2016-06-01 17:45:54 cri
Kungiyar kwallon kafar Real Madrid ta Sifaniya ta gudanar da bikin murnar daukar kofin zakarun turai karo na 11, a ranar Lahadin karshen mako. Da fari dai kungiyar ta isa babban dakin taron jama'a ne kafin kuma ta kewaya wasu babban birnin kasar, aka kuma kammala da babban biki a filin wasa na Bernabeu.

A wasan karshe da kungiyar ta buga da takwarar ta ta Atletico Madrid sun tashi ne kunnen doki daya daya, sana'an nan aka buga bugun da ga kai sai mai tsaron gida, a kuma wannan gaba ne Real Madrid ta samu nasara kan abokiyar karawar ta.

Duk dai da cewa an samu saukar ruwan sama a daren ranar ta Lahadi, hakan bai hana dubban masoya kungiyar jiran tawagar 'yan wasan ba. Kafin haduwa da masoyan kungiyar, sai da jami'an ta, da 'yan wasan Real din suka gabatar da kofin ga magajin garin Madrid Manuela Carmena, da kuma shugabar kungiyar masoyan ta Cristina Cifuentes.

Bayan kammala hakan ne kuma 'yan wasan, da kocin su Zinedine Zidane, tare da shugaban kungiyar Florentino Perez suka koma filin wasa na Bernabeu, inda aka yi gagarumin biki tare da wasan wuta domin nuna farin ciki ga wannan nasara ta kungiyar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China