Mataimakin minista mai kula da ayyukan bunkasa rayuwar al'umma na kasar ta Sin Xin Changxing ne ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin wani taron manema labarai. Ya ce alkaluman samar da guraben ayyukan yi na kan madaidaicin mizani, ko da yake akwai rashin daidaito a fannin ma'aikatan da sassa daban daban ke bukata.
Mr. Xin ya bayyana cewa bukatar ma'aikata daga kamfanoni ko masana'antu masu manyan ayyuka na raguwa, yayin da bukatar hakan daga kamfanonin dake neman ma'aikata masu kwarewa mai zurfi ke karuwa.
Jami'in ya kuma jaddada burin gwamnatin kasar Sin, na samar da karin guraben ayyukan yi ga al'ummar kasar, musamman duba da yadda miliyoyin ma'aikata ke fuskantar karancin abun yi a wuraren ayyukan su, sakamakon gyare gyare da ake yi ga tsarin manasan'antu da kamfanoni, yayin da kuma sauke nauyin ma'aikata ke zame wa karin masana'antu da kamfanoni kalubale.