Kwalejin na Lausanne da ke kasar Switzerland ya yaba gogayyar yankin Hong Kong na Sin, yana mai imanin cewa, yankin Hong Kong na da ingantattun tsarin bankuna da hada-hadar kudi, da manufofin da za su karfafa kirkire-kirkire, da tsarin biyan haraji mai kyau. Ban da wannan kuma, yankin na Hong Kong ya yi fice wajen gudanar da kasuwanci, shi ya sa tattalin arzikin yankin ya samu bunkasuwa sosai.(Bako)