in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire: Sojojin MDD uku sun mutu a cikin wani hadarin mota
2016-05-31 13:23:51 cri
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Cote d'Ivoire ONUCI ta bayyana cewa, sojojin MDD uku 'yan asilin kasar Senegal na tawagar sun mutu a lokacin da suke aikin sintiri, bayan motarsu ta yi wani hadari,.

Sojojin wanzar da zaman lafiya dake gudanar da wani aikin sintiri ne, a lokacin, bisa wasu dalilan da har yanzu ba a hakikance ba, motar da suke ciki ta jirkice.

Mutuwar tasu ta kai ga yawan dakarun MDD 104 da suka mutu tun farkon aikin tawagar MDD a cikin watan Afrilun shekarar 2004 a wannan kasa.

MDD ta shiga a kasar Cote d'Ivoire a karkashin wata tawagar wanzar da zaman lafiya bayan rikicin siyasa da ya barke a shekarar 2002, wanda a lokacin ya hada sojojin gwamnati da 'yan tawaye dake dauke da makamai.

A halin yanzu tawagar MDD na aikin maido da zaman jituwa tsakanin al'ummomin kasar, tun bayan rikicin zabe na shekarar 2002 zuwa 2011.

ONUCI ta kaddamar da shirin rage dakarunta, kuma tawagar na shirin kammala aikinta a cikin watan Junin shekarar 2017. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China