in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ba da lambar yabo ga rukunin 'yan sandan kwantar da tarzoma na 3 da kasar Sin ta tura kasar Liberiya
2016-05-31 11:13:29 cri

A jiya Litinin a birnin Jinan na lardin Shandong na kasar Sin, an yi bikin ba da lambar yabo ga rukunin 'yan sandan kwantar da tarzoma na 3 da kasar Sin ta tura kasar Liberiya. Kana ma'aikatar tsaro ta kasar Sin ta ba da lambobin yabo na farko na aikin soja ga wannan rukuni.

Wannan rukuni ya shiga kasar Liberiya don gudanar da aiki daga watan Maris na shekarar 2015, bayan wa'adin aikinsa na kusan shekara guda, ya kammala aiki da komawa gida a watan Maris na shekarar 2016.

Kwamishinan hukumar kula da harkokin tsaron iyakar kasa ta ma'aikatar tsaro ta kasar Sin Mou Yuchang ya bayyana cewa, rukunin 'yan sandan Sin sun kammala ayyukan yin sintiri da ba da kariya da daidaita rikici da kuma sauran ayyukan kiyaye zaman lafiya a yayin da suke fama da ayyuka masu dimbin yawa da yaduwar cutar Ebola da kuma rashin kyakkyawan muhallin zaman rayuwa da dai sauransu.

Kwamishinan rukunin 'yan sandan kwantar da tarzoma Li Peisen ya bayyana cewa, rukunin musamman na MDD ya mai da tsarin hadin gwiwar 'yan sanda da sojoji da tsarin mai da martani ga batutuwan gaggawa da wannan rukuni ya kirkiro a matsayin abin koyi, kuma a karo na farko ya gabatar da wannan tsarin kasar Sin a yayin da ake horar da darektoci masu kula da aikin kwantar da tarzoma a MDD.

Sabo da kyawanwan ayyukan da rukunin 'yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Sin ya kammala, MDD ta ba da lambobin yabo na kiyaye zaman lafiya ga dukkan membobi 140 na wannan rukuni.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China