in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in M.D.D. yana fatan kasashe da dama za su more fasahohin da kasar Sin ta samu
2016-05-31 09:57:16 cri
Mai ba da shawara na musamman ga sakatare janar na M.D.D. game da shirin samun dauwamammen ci gaba ya zuwa shekarar 2030 David Nabarro ya bayyana a Nyingchi dake jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin cewa, yana fatan kasashe da dama za su yi amfani da fasahohin da kasar Sin ta samu, don gaggauta samun ci gaba.

Nabarro ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da ya shugabanci wata tawagar M.D.D. don halartar taron kara-wa-juna-sani na kasa da kasa game da shirin samun dauwamammen ci gaba na shekarar 2030. Ya ce, kasar Sin ta taka rawar gani game da inganta hadin gwiwa a tsakaninta da kasashe masu tasowa, yana fatan Sin za ta taimakawa sauran kasashe amfana da fasahohin da ta samu. Game da wasu fannoni, Sin ta ba da babbar gudummawa.

A yayin taron koli game da samun ci gaba cikin dogon lokaci da aka shirya a ranar 25 ga watan Satumbar bara, M.D.D. ta fidda shirin samun dauwamammen ci gaba na shekarar 2030, inda aka tsaida kudurin kawar da talauci da rashin daidaito, da warware batun sauyin yanayi. A bisa tushen shirin muradun karni da aka tsara a shekarar 2000 wato MDGs, an tsaida wannan sabon kudurin, wanda ke kunshe da dukkan kasashe daban daban, ba ma kawai kasashe masu fama da talauci ba, don tabbatar da cewa, za a sanya dukkan mutanen duniya amfana da shirin samun ci gaba.

Nabarro ya ce, wannan shiri ya shafi makomar kasashen duniya, don haka idan ba a shigar da gwamnatin Sin da jama'arta ba, ba za a cimma wannan buri ba. Ba ma kawai saboda tattalin arzikinta yana da karfi a duniya ba, Sin ta yi fice game da rage talauci da sauransu. Dadin dadawa kuma, yayin da gwamnatin Sin ta tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13, ban da raya tattalin arziki, Sin ta dukufa ka'in da na'in wajen kiyaye muhalli, da rage rashin daidaito a duniya, hakika, Sin ta kafa wani misali mai kyau wajen samun ci gaba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China