in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta buga wasannin sada zumunta da Mali da Luxembourg
2016-05-11 16:43:40 cri

Mai rike da mukamin kociyan kungiyar Super Eagles ta Najeriya Salisu Yusuf, ya ce kungiyar za ta buga wasannin sada zumunta biyu nan gaba cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Wasannin dai sun hada da Najeriya da Mali wanda za a buga a kasar Faransa, tuni kuma aka gayyaci 'yan wasan Najeriyar su 26 domin bugawa Super Eagles din wannan wasa.

Kaza lika Najeriyar za ta buga wani wasan na sada zumunta da kasar Luxembourg a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa. Kocin kungiyar ya ce koda yake tawagar kungiyar na kunshe da tsaffin 'yan wasan ta, amma duk da hakan za a baiwa matasan 'yan wasa damar nuna ta su basirar a yayin wasannin.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China