in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibiya ta fara shirye shiryen shiga gasar wasanni kwallon kafa a Ghana
2016-05-11 16:32:48 cri
Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Namibiya (NFA) ta tura 17 daga cikin 'yan wasan kasar domin basu horo na musamman a birnin Accra na kasar Ghana, daga ranakun 10 zuwa 23 ga watan Mayun wannan shekara a shirye shiryen gasar wasannin kwallon kafa dake tafe.

A cewar sakatare janar na kungiyar NFA Barry Rukoro, kaciyan 'yan wasan Ricardo Mannetti ne ya zabo 'yan wasan bayan kammala wasan sada zumanta na cikin gida.

Yan wasan zasu tashi zuwa kasar ta Ghana ne, kuma zasu samu horo na musamman domin shiga gasar wasannin share fage ta AFCON 2017 inda zasu kara da Niger a ranar 4 ga watan Yuni da kuma gasar COSAFA Castle Cup tsakanin ranakun 18 zuwa 25 ga watan Yuni.

Da safiyar ranar Talata ne dai tawagar 'yan wasan ta tashi zuwa kasar Ghana, inda ake saran dawowarsu a ranar 23 ga watan Mayu, inda zasu hadu da sauran 'yan wasannin kungiyar dake zaune a kasashen ketare domin samar da babban kungiyar 'yan wasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China