in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da ministan harkokin wajen kasar Japan
2016-05-01 13:08:48 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da ministan harkokin wajen kasar Japan Kisida Fumio dake ziyara a nan kasar Sin a ranar 30 ga watan Afrilu da yamma.

A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, raya dangantakar dake tsakanin Sin da Japan yadda ya kamata a dogon lokaci ya dace da moriyar kasashen biyu da jama'arsu, kana zai taimakawa kiyaye zaman lafiya da samun wadata a yankin har ma a dukkan duniya. A shekarun baya baya nan, dangantakar dake tsakanin Sin da Japan ba ta samu ci gaba yadda ya kamata ba. A halin yanzu, ana kokarin kyautata dangantakarsu, amma babu tushe mai karfi wajen haka, saboda haka ya kamata kasashen biyu su bi hanya mafi dacewa wajen raya dangantakarsu. Kasar Sin tana son bin tunanin "koyi fasahohi daga tarihi domin hangen makoma", da yin kokari tare da kasar Japan don kara yin imani da juna a fannin siyasa da sa kaimi ga raya dangantakarsu yadda ya kamata.

A nasa bangare, Kisida Fumio ya bayyana cewa, Japan tana son bin tunanin takardu 4 na siyasa da Sin da Japan suka daddale, da tsaya tsayin daka kan manufar "kasancewar abokan hadin gwiwa da ba tare da kawo barazana ga juna ba", da kuma girmama juna da kara yin imani da juna da kuma warware matsalolin dake tsakaninsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China