in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fitar da doka ta farko kan kungiyoyi masu zaman kan su na ketare dake Sin
2016-04-29 10:59:13 cri

Jiya Alhamis da yamma, hukumar tsara dokokin kasar Sin, wato zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar Sin, ya zartas da dokar da za ta tafiyar da harkokin kungiyoyi masu zaman kan su ko NGO na kasashen waje dake nan kasar Sin, wannan doka ita ce irin ta ta farko da gwamnatin kasar Sin ta tsara, domin tafiyar da harkokin irin wadannan kungiyoyi na ketare dake aiki a kasar Sin, wadda ta tanaji kiyaye moriya da hakkin su bisa doka. To ko ina dalilin da ya sa kasar Sin kafa irin wannan doka? Ko hakan yana nufin cewa, gwamnatin kasar Sin za ta rufe kofar ta ga kungiyoyi masu zaman kan su na ketare?

Tun bayan da aka fara bude kofa ga kasashen waje, da kuma gudanar da kwaskwarima a kasar Sin a cikin shekaru sama da talatin da suka gabata, adadin kungiyoyi masu zaman kan su na kasashen waje, wadanda ke gudanar da harkokinsu a kasar Sin ya karu sannu a hankali. Bisa alkaluman kididdigar da aka fitar, a halin da ake ciki yanzu, adadin wadannan kungiyoyi ya riga ya kai kusan dubu goma. Domin tafiyar da ayyukansu a kasar Sin, tare kuma da kiyaye moriya, da hakkin su bisa doka, ya zama wajibi a tsara dokar da ke shafar hakan.

Mataimakin darektan kwamitin kula da harkokin dokoki, na zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar Sin Zhang Yong ya bayyana cewa, "Gwamnatin kasar Sin na maraba da zuwan NGO na ketare don su gudanar da ayyukansu a kasar Sin, kuma tana nuna kwazo da himma kan cudanya da hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu, amma sai dai abun takaici ne yadda wasu kungiyoyi masu zaman kan su na kasashen waje, ke makarkashiyar kawo barna, ko sun riga sun kawo barna ga kwanciyar hankalin zamantakewar al'ummar kasar Sin, da tsaron kasar ta Sin. A saboda haka, wajibi ne a tafiyar da harkokin kungiyoyin bisa doka."

Bisa dokar da aka tsara, hukumar kula da kwanciyar hankalin jama'a ta kasar Sin, za ta kula da ayyukan dake shafar irin wadanan kungiyoyi na ketare. Alal misali batun yi musu rajista, da bincike na shekara shekara, da kuma gabatar da shiri game da aikin su a kasar Sin, kana da batun hukunta su idan suka gudanar da ayyukan da suka sabawa doka a kasar Sin.

Kan wannan, mai sa ido kan aikin dokar kwanciyar hankalin jama'a na kwamitin kula da harkokin dokoki, na zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar Sin Guo Linmao ya bayyana cewa, hukumar kula da kwanciyar hankalin jama'a ta kasar Sin tana sauke nauyin kiyaye tsaron kasa da tsarin zamantakewar al'umma, tare kuma da hana aikatawar laifuffuka da kuma hukunta wadanda suka aikata laifuffuka, kana tana sauke nauyin tafiyar da harkokin samun izinin zama a kasar Sin da harkokin dake shafar shigowa kasar Sin daga ketare, da fita zuwa ketare daga kasar Sin, ban da haka kuma, tana kula da ayyukan 'yan asalin kasashen waje a kasar ta Sin. Kan wannan, Guo Linmao ya bayyana cewa, "Idan aka gano laifuffukan da ake aikatawa, hukumar kula da kwanciyar hankalin jama'ar kasar Sin za ta dauki matakai nan take, kuma bisa doka. Ke nan idan ba a aikata laifuffuka ba, babu bukatar jin wani tsoro."

Wasu mutane suna zaton cewa, gwamnatin kasar Sin ta zartas da wannan doka kan NGO na ketare ne domin kayyaden ayyukansu a kasar, wasu kuwa suna cikin zulumin cewa, ko kila gwamnatin kasar Sin za ta hana shigowar wasu kungiyoyi masu zaman kan su na ketare, da ke mai da hankali kan hakkin dan Adam a kasar ta.

A yayin taron manema labaran da aka shirya jiya, mai sa ido kan aikin dokar kwanciyar hankalin jama'a, na kwamitin kula da harkokin dokoki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar Sin Guo Linmao ya bayyana cewa, "Muna maraba ga zuwan kungiyoyi masu zaman kan su na ketare a kasarmu, muna maraba da zuwan NGO na ketare da alaka da hakkin dan adama, kuma za mu samar da damammaki gare su domin yin hadin gwiwa da cudanya, kana za mu kiyaye moriya da hakkinsu bisa doka, amma idan suka aikata laifuffuka, za mu hukunta su nan take. A takaice dai, muna bude kofa ga dukkan NGO na ketare da suke gudanar da ayyukansu bisa doka a kasar Sin."

Wannan doka za ta fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2017, yanzu haka ana yin nazari domin fitar da wasu hakikanin sassa dake shafar aikin tafiyar da harkokin NGO na ketare cikin sauri, kuma za a sanar su ga sassan da abin ya shafa ta shafin yanar gizo a lokacin da ya dace, ta yadda za a ba da jagoranci ga NGO na ketare, wadanda za su gudanar da ayyukansu a kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China