in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulub din kwallon kafa na Argentina yana da kyakkyawan tsammani a gasar Rio 2016
2016-04-28 15:12:12 cri
Bisa ga jerin sunayen 'yan wasan na baya bayan nan kimanin 57 wanda ake saran wallafawa a yan kwanaki masu zuwa, kungiyar wasan kwallon kafa ta Argentinean ta fara shirye shiryen karbe lambar yabo ta zinare a gasar wasannin Olympic.

Baya ga samun lambobin yabo na zinare har sau biyu wato a Athens a 2004, da kuma Beijing a 2008, sannnan da lambar yabo ta azurfa a Amsterdam a 1928 da Atlanta 1996, ana saran tawagar kulub din yan wasan na Argentina zata iya kasancewa a sahun farko a gasar wasannin.

Kociyan kungiyar Gerardo Martin, yana tsaka mai wuya wajen zakulo 'yan wasan da suka fi dacewa, wadan da suka fi kwarewa domin cimma muradun kungiyar wasan. Sai dai baya ga wannan kuma, yan wasa Lionel Messi, da Sergio Aguero da kuma Angel di Maria, Martin ya bayyana cewar za'a baiwa fitattun matasan 'yan wasan dama a wasan na Rio domin su taka leda, musamman a yayin da ake shirye shiryen tunkarar gasar kwallon kafa ta duniya a 2018 a kasar Rasha.

Zuwa ranar 1 ga watan Yuni, Martin zai ayyana jerin sunayen yan wasan 35, sai kuma bayyana sunayen 'yan wasan 18 na kasar a ranar 14 ga watan Yuli.

Ga kasar wacce ta jima bata samu muhimmiyar lambar yabo ta kasa da kasa ba tun bayan ta Copa America a shekarar 1993, ana saran wannan gasar wasannin na Olympics ya kasance a matsayin wata babbar dama da kasar zata yi amfani da ita.

Duk da cewar tauraron kungiyar wasan ya dan disashe a gasar wasannin kwallon kafa na duniya na baya bayan nan, sai dai har yanzu, Argentina tana tuna bajintar data nuna a gasar wasannin ta Beijing a 2008 wanda a lokacin ne shahararran matashin dan wasan Lionel Messi, ya ciwowa kasar Argentina lambar yabo ta zinare. Wannan nasara na daya daga cikin abinda ya haskaka tauraron Messi a duniya, wanda ya taimakawa kasar ta samu nasarar zara kwallaye 3 da nema tsakaninta da Brazil a wasan kusa dana karshe, sai kuma a wasan karshe inda suka jefa kwallo 1 mai ban haushi a wasanta da Najeriya a katafaren filin wasa na Beijing.

Shekaru 4 kafin wannan, wanda Marcelo Bielsa ya gudanar karkashin jagorancin Carlos Tevez, Argentina ta samu nasarar lashe lambar yabo na zinare na kwallon kafa a karon farko a shekarar 2004.

Koda yake kafin wannan ta taba samaun lambar yabo ta azurfa a Amsterdam a 1928, sai dai Argentina ta fafata a wasan kusa dana kusan karshe a Rome a 1960, sai kuma a zagayen farko a Tokyo a 1964, sai wasan kusa da na kusan karshe a Seoul 1988 kafin zuwa wasan karshe a Atlanta a 1996, inda ta bada mamaki bayan da Najeriya ta lallasata da ci 3 da 2.

Ana gananin wasannin Olympic na wasannan shekara a matsayin wata dama ce ga Argentina inda zasu fafata da Brazil.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China