in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nuna motocin da ke amfani da makamashi mai tsabta a bikin nune-nunen motocin Beijing na 2016
2016-04-28 11:57:31 cri

A halin da ake ciki yanzu, ana gudanar da nune-nunen motocin kasashen duniya na shekarar 2016 a cibiyar nune-nunen birnin Beijing. A yayin nune-nunen da ake gudanarwa, motocin da aka kera masu amfani da fasahar zamani sun fi jawo hankalin jama'a, to, ko ana iya cewa, za a fara amfani da irin wadannan motoci a maimakon motoci na yanzu?

Babban taken bikin nune-nunen motocin kasashen duniya na shekarar 2016 da ake gudanarwa a nan Beijing shi ne "kirkire-kirkire da kwaskwarima", daga wannan take, ana iya gano cewa, za a gabatar da motocin da ake tukawa ta hanyar amfani da sabon makamashi mai tsabta. A yayin nune-nunen na wannan karo, gaba daya an gabatar da motoci kusan 1200, a cikinsu, adadin motocin da ke amfani da sabon makamashi mai tsabta wato lantarki, ko gaurayen lantarki da mai, ya kai wajen kashi 20 cikin dari, adadin da ya kai matsayin koli a tarihin bikin nune-nunen motocin.

Mai ba da taimako ga babban manajan kamfanin kera mota na BYD Du Guozhong ya yi mana bayani da cewa, "Ana iya cewa, manufar ci gaban fasahar kera mota yana da kyau matuka, kuma ana sayar da motocin da ke amfani da sabon makamashi mai tsabta lami lafiya, karkashin taimakon manufar gwamnatin kasar ta Sin, inda a shekarar bara, adadin wannan nau'i na motocin da aka sayar ya kai dubu 330. Ban da haka kuma, bisa shirin da gwamnatin kasar ta tsara, an ce, za a kara sayar da irin wannan mota har adadin su ya kai miliyan 5 kafin karshen shekarar 2020. A ko wace shekara, adadin zai karu bisa babban mataki, kuma ko shakka babu, makomar kasuwar sayar da motocin tana da haske sosai."

Bisa alkaluman kididdigar da aka fitar a shekarar 2015, adadin motocin dake amfani da mai iri na gargajiya da aka sayar da su a kasar Sin ya kai wajen miliyan 20, wato adadin motocin dake mafani da sabon makamashi mai tsabta bai kai kashi 2 cikin dari ba, amma abu mafi muhimmanci shi ne motocin dake amfani da sabon makamashi mai tsabta da kamfanonin kasar Sin ke kerawa sun samu ci gaba cikin sauri, dalilin da ya sa haka shi ne, domin ana amfani da sabbin fasahohin kera motocin, kuma ana yin kirkire-kirkire kan aikin su.

A halin da ake ciki yanzu, motocin dake amfani da sabon makamashi mai tsabta da kamfanonin kasar Sin suke kerawa suna iya tafiya har tsawon kilomita 400 idan aka cika su da lantarki, ana iya cewa, an kai matsayin koli a duniya. Ban da haka, idan aka kara yawan wuraren samar da lantarki gare su, to, ko shakka babu motocin dake amfani da makamashi mai tsabta za su samu ci gaba yadda ya kamata, kuma za su samu ci gaba cikin sauri.

Kan wannan batu, mataimakin babban manajan kamfanin kera mota na Chery na kasar Sin Fan Xing ya bayyana cewa, "Amfani da sabon makamashi mai tsabta wajen kera motoci sabon kuduri ne a wannan fanni bisa dalilai na kare muhalli, ya zuwa shekarar 2020, adadin zai karu da kashi 10 cikin dari, muna cike da imani kan makomar kasuwar irin wadannan motoci."

Kaza lika, game da mota mai tuka kan ta kuwa, a baya ana iya kallon irin wadannan motoci ne kawai a sinima, amma yanzu wadannan motoci sun fara shiga rayuwar yau da kullum ta al'umma.

A yayin bikin nune-nunen bana a nan Beijing, an yi nune-nunen irin wadannan mota masu tuka kan su.

Game da wannan, shugaban kamfanin kera mota na Boshi na kasar Sin Chen Yudong ya bayyana cewa, irin wannan sabuwar fasaha za ta kawo sabuwar hanyar zaman rayuwa gare mu. Ya ce, "Mota mai tuka kan ta za ta kara yin tasiri ga zaman rayuwar matuka, saboda muna bukatar sabbin fasahohi domin kara kyautata ingancin zaman rayuwarmu. Ina ganin cewa, fasahar kera mota mai tuka kan ta za ta samu babban ci gaba cikin shekaru goma masu zuwa."

A yayin bikin nune-nunen motocin bana, wata mota da ake kira "motar yanar gizo" wato motar da aka kera da fasahar zamani, ta fi jawo hankalin jama'a, manajar kula da aikin tallar motar Cui Yali ta bayyana cewa, "Yanar gizo na yin babban tasiri ga zaman rayuwar jama'a, shi ya sa kamata ya yi hakan ya kawo tasiri ga motoci, misali fannin sarrafa mota ta hanyar amfani da yanar gizo, yanzu kamfanonin kera motoci na kasar Sin suna kokari matuka kan wannan aiki, don haka suke samun ci gaba yadda ya kamata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China