160428-Ghana-za-ta-kara-da-habasha-a-gasar-kwallon-kafa-ta-yan-kasa-da-shekaru-20-zainab.m4a
|
Tuni dai Habasha ta doke Somalia da jimillar kwallaye 4 da 1, bayan kammala wasan su na Juma'ar da ta gabata, inda kuma za su fafata da Black Satellites ran 20 ga watan Mayu a birnin Addis Ababa a wasan farko, kana su sake haduwa a wasa na biyu ran 10 ga watan Yuni a birnin Accra. Duk kungiyar da ta yi nasara a wannan wasa kuma za ta hadu da ko dai Tunisia ko Senegal a wasa na gaba.
Kungiyoyi 7 da suka shige gaba, za su kece raini a gasar zakarun nahiyar da za ta gudana tsakanin ranekun 26 da watan Fabarairu zuwa 12 ga watan Maris na shekarar mai zuwa a Zambia. Kaza lika kungiyoyin da suka kai ga wasan kusa da na kusan karshe su 8, su ne za su wakilci nahiyar a gasar duniya ta shekarar 2017, ta 'yan kasa da shekaru 20 wadda hukumar FIFA ke shiryawa.
A bara Ghana ce ta uku yayin gasar nahiyar ta Afirka wadda ta gudana a kasar Senegal. (Saminu Alhassan)