A yau Laraba da karfe 2 na safe agogon kasar Sin, cibiyar nazarin kimiyyar sararin samaniyya ta kwalejin koyon ilmin kimiyyar kasar Sin ta harba wata rokar nazari mai suna kunpeng-1B a birnin Danzhou da ke lardin Hainan na kasar Sin, an gudanar da ayyukan gwaje-gwaje da dama na harba wannan roka, inda aka samun cikakkiyar nasara a wannan aiki.
An yi amfani da fasahohin zamani wajen harba wannan roka, gami da wasu alkaluman lissafi, lamarin da ke da ma'anar musamman game da nazarin sararin samaniyya.(Bako)