A gun bikin karramawar, mataimakin wakilin babban sakataren MDD mista Valdemar ya nuna babban yabo ga 'yan sandan kasar Sin kan ladabtarwa da kyakyawar fasaha a fannin aiki da suke da su.
A lokacin da 'yan sandan rukunin kiyaye zaman lafiya na 14 na kasar Sin suke aiki a kasar Liberia, sun yi kokarin aiki a fannonin kiyaye zaman lafiya, da yin bincike, da yaki da miyagun kwayoyi, da kuma sauransu, a daidai lokacin da aka fuskanci kalubalen cutar Ebola. Ban da haka kuma, sun kare moriyar Sinawa da kuma kamfannonin Sin a can yadda ya kamata, sun ba da muhimmiyar gudummowa wajen kiyaye zaman lafiya a kasar Liberia da inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Liberia.(Lami)