in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Najeriya ya yi tsokaci kan ziyarar da shugaba Buhari zai yi a Sin
2016-04-11 10:43:36 cri

Zumuncin dake tsakanin Sin da Najeriya yana da dogon tarihi, kuma yana kara zurfafuwa a kwana a tashi. Kasar Sin kasa mafi girma ce mai tasowa, Najeriya ita ma kasa ce mafi girma a nahiyar Afirka, wadda ke da yawan al'umma da kuma matsayin tattalin arziki. Kasashen biyu suna mallakar wayewar kai da al'adun da ake alfahari kan su, a sa'i daya kuma, suna fuskantar matsala a fannin neman samun ci gaba. Duk wadannan abubuwan da suke yin kama da juna da kasashen biyu ke da su sun aza harsashe mai karfi ga hadin gwiwa tsakanin su. Kana shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 45 da kafa huldar diplomasiya tsakanin kasashen biyu, a cikin wadannan shekaru 45, huldar dake tsakanin su ta samu bunkasuwa yadda ya kamata a karkashin kokarin da shugabannin kasashen biyu suke yi, har ma an samu babban sakamako wajen hadin gwiwa a fannoni daban daban dake tsakanin su.

Najeriya babbar aminiya ta Sin ce a fannin hadin gwiwar tattalin arziki a nahiyar Afirka, sassan biyu wato Sin da Najeriya sun samu babban ci gaba yayin da suke gudanar da hadin gwiwa a fannonin ciniki da aikin gona da makamashi da gine-ginen more rayuwar jama'a da sadarwa da sauran su. Kafin shekaru 45 da suka gabata, adadin cinikin dake tsakanin sassan biyu a ko wace shekara ya kai dalar Amurka miliyan 10 kawai, amma yanzu adadin ya riga ya zarce dalar Amurka biliyan 10. Kana a cikin 'yan shekarun da suka gabata, Najeriya ta kasance kasuwa mafi girma ta kasar Sin da kamfanoninta ke gudanar da ayyukan gina gine-gine a kasashen Afirka, kuma ta kasance babbar kasuwa ta biyu da kamfanonin kasar Sin ke fitar da kayayyaki zuwa Afirka, kana ta kasance babbar aminiyar ciniki ta uku ta kasar Sin a Afirka. Ya zuwa karshen shekarar 2015, gaba daya adadin jarin da ba na kudi ba da kasar Sin ta zuba kai tsaye a Najeriya ya kai sama da dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 500. Kazalika, ana gudanar da wasu manyan ayyuka kamarsu harbar tauraron dan adam da gina layin dogo a Najeriya yadda ya kamata.

A fannin cudanyar al'adu kuwa, sassan biyu su ma sun samu babban sakamako, misali, tun tuni kasar Sin ta kafa cibiyar al'adun Sin a Najeriya, Najeriya ita ma ta kafa cibiyarta ta al'adu a kasar Sin, ko wace shekara, kasashen biyu su kan shirya ayyuka iri iri domin yin musanyar al'adu, ta yadda za a sa kaimi kan fahimtar juna tsakanin al'ummomin kasashen biyu. Kawo yanzu kasar Sin ta riga ta kafa kwalejojin koyar da Sinanci ta Confucius guda biyu da sauran cibiyoyin koyar da Sinanci guda hudu a Najeriya, al'ummar Najeriya, musamman ma matasan kasar suna sha'awar koyon Sinanci kwarai, har wasu daga cikin su sun zo nan kasar Sin domin kara samun ilmi, ana iya cewa, cudanya tsakanin al'ummomin kasashen biyu ta samu ci gaba a bayyane.

Wajen hadin gwiwar tattalin arziki kuwa, kasashen biyu suna da babban karfi a asirce, saboda Najeriya tana da albarkatun hallitu masu arziki, kuma tana da yawan al'umma, shi ya sa ta kasance babbar kasuwa, kasar Sin tana da jari da fasaha da Najeriya ke bukata, a saboda haka, sassan biyu suna gudanar da hadin gwiwa a fannoni daban daban yadda ya kamata. Ban da haka, Sin da Najeriya suna fuskantar matsalar tsaro, shi ya sa suna fatan za su kara karfafa hadin gwiwa a wannan fanni tsakanin su, kuma suna son kara karfafa cudanya da sulhuntawa kan wasu manyan batutuwan kasa da kasa domin kiyaye moriyarsu da kuma moriyar sauran kasashe masu tasowa.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, manyan jami'an Sin da Najeriya suna kai wa juna ziyara a kai a kai, amincin siyasa dake tsakanin kasashen biyu shi ma ya kara karfafa lami lafiya. Tun bayan watan Mayun bara wato bayan da shugaba Buhari ya hau kan kujerar shugaban kasar Najeirya, shugabannin biyu wato Xi Jinping da Buhari su ma sun yi ganawa sau da dama, a yayin ganawar da suka yi, sun yi musanyar ra'ayoyi kan hadin gwiwa tsakanin kasashen su, kuma sun cimma matsaya guda daga duk fannoni.

Kamar yadda aka sani, hadin gwiwa yana da muhimmanci, muddin dai sassan biyu wato Sin da Najeriya suna yin hadin gwiwa yadda ya kamata, to za su samu makoma mai haske.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China