Jami'in hukumar kwallon fata na kasar NFF Mohammed Sanusi, ya ce shirye shirye sun yi nisa don kammala shirin bada horon.
Game da shirye wasannin FIFA na mata yan kasa da shekaru 17, wanda za'a gudanar a kasar Jordan a nan gaba cikin wannan shekara, Sanusi ya ce, sun kai babban mataki game da shirye shiryen shiga wasannin.
Yace, zasu samar da kyakkyawan yanayi da kayayyakin da ake buka ga 'yan wasan, sai dai yace sauran shirye shirye ta fuskar tsare tsare yana karkarin ikon kociyan kungiyar wasa na kasar.(Ahmad Fagam)