in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na fatan cimma karin nasarori a gasar Olympic ajin nakasassu ta bana
2016-04-06 16:13:54 cri
Shugaban hukumar gudanarwa, ta wasannin motsa jiki ajin nakasassu ta Najeriya ko NPC Monday Emoghavwe, ya ce hukumar sa na daukar matakan duk da suka kamata, domin tabbatar da cewa kasar ta samu karin nasarori a gasar dake tafe cikin wannan shekara a kasar Brazil.

Ya ce za su tabbatar sun kimtsa 'yan wasan da za su wakilci kasar yadda ya kamata, ta yadda hakan zai baiwa kasar damar samun karin lambobin yabo sama da wadanda ta samu a shekara ta 2012.

Mr Emoghavwe wanda ya shaida hakan ga mane ma labarai a birnin Ikkon jihar Legas, ya ce da zarar kudaden da ake bukata sun shiga hannun hukumar ta NPC, za su tara 'yan wasan kasar domin basu karin horo.

Daga nan sai ya yi kira ga sassa masu zaman kan su, da su tallafawa kwazon gwamnatin kasar, wajen daukar nauyin horas da 'yan wasan na Najeriya.

A yayin gasar da ta gudana a birnin landan a shekarar 2012, Najeriya ta lashe lambobin zinari 6, da azurfa 5 da kuma tagulla 1. A bana kuwa za a gudanar da wannan gasa wadda Brazil za ta karbi bakunci ne tsakanin ranekun 7 zuwa 18 ga watan Satumbar dake tafe.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China