160331-murtala.m4a
|
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya, gami da ma'aikatar harkokin masana'antu, cinikayya da zuba jari ta tarayyar Najeriya su ne suka shirya wannan dandalin tattaunawa. Manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu, ciki har da jakadan kasar Sin dake Najeriya Mista Gu Xiaojie, da karamar ministar masana'antu, cinikayya da zuba jari ta Najeriya Hajiya A'isha Abubakar.
A yayin tattaunawar, jami'an kasashen Sin da Najeriya, da wasu shugabannin kamfanonin Sin dake Najeriya, da kuma jagororin kungiyoyin 'yan kasuwan Najeriya da dama suka tofa albarkacin bakinsu game da yadda za su yi domin karfafa hadin-gwiwa a fannin kasuwanci da zuba jari.